Hadimin Shugaban kasa ya bayyana inda aka kwana game da batun ‘takarar’ Osinbajo

Hadimin Shugaban kasa ya bayyana inda aka kwana game da batun ‘takarar’ Osinbajo

  • Babafemi Ojudu ya yi magana a kan rade-radin da ke yawo game da takarar Farfesa Yemi Osinbajo
  • Hadimin shugaban kasar ya ce Yemi Osinbajo zai bayyana matsayarsa game da neman shugabanci
  • ‘Yan siyasa su na ta dandazo su na zuwa ofishin Ojudu domin jin ko Osinbajo zai fito takara a 2023

FCT, Abuja – Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu ya tanka masu rade-radin cewa Yemi Osinbajo zai yi takara.

Tun tuni ake ta jita-jitar cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai nemi tikitin takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar APC a 2023.

Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Babafemi Ojudu yace ‘yan siyasa da-dama su na ta zuwa ofishinsa domin jin ko Osinbajon zai tsaya takara.

Legit.ng Hausa ta samu labari hadimin na Muhammadu Buhari ya yi wannan magana ne a shafin Facebook a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022.

Kara karanta wannan

Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

Mai ba shugaban Najeriyar shawara ya ce Farfesa Osinbajo zai amsa wannan tambaya da ake ta yi.

Mataimakin Shugaban kasa
Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: @ProfOsinbajo
Asali: Facebook

“Ofishina ya zama Makkar ‘yan siyasa. Yau manyan ‘yan siyasar Kano; Dr Kabir Nakaura da Farfesa Hafiz Abubakar ne suka kawo mani ziyara.
“Dr. Nakaura amini ne kuma abokin karatun Marigayi shugaban kasa Umaru Yar’Adua tun daga firamare har jami’a.”
“Farfesa Hafiz Abubakar kuma ya yi mataimakin gwamna a jihar Kano.”
“Abin da kowa yake tambaya shi ne shin Osinbajo zai yi takara ko ba zai yi ba. Za a ji amsar wannan tambaya ba da dadewa ba.”

- Babafemi Ojudu

Mutane su na ta magana

Tuni irinsu Farfesa Farouk Kperogi suka fara maganganu, suka ce ba zai yiwu Najeriya ta fito daga hannun Buhari, ta fada wajen Tinubu ba, yace shi kan shi Osinbajo bangare ne na gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Najeriya 7 da ke harin shugabancin kasa a zaben 2023

Timawus Mathias kuma yace kuskure Bola Tinubu zai tafka a wannan gaba idan bai kyale Osinbajo ya karbi ragamar mulki ba, yace hakan zai dunkule kasar Yarbawa da Najeriya.

Aliyu Nuhu kuwa yace babu wanda ya cancanta ya zama magajin Buhari sai mataimakinsa Osinbajo wanda aka yi shekara takwas da shi a gwamnati ba tare da matsala ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel