Rigingimun cikin gidan APC su na kara ta’azzara yayin da za a shiga shekarar neman zabe

Rigingimun cikin gidan APC su na kara ta’azzara yayin da za a shiga shekarar neman zabe

  • Ba a ga macijin tsakanin yaran Muhammad Danjuma Goje da na Gwamna Inuwa Yahaya a Gombe
  • A jihar Anambra ma ana ta rigima a kan wanda zai rike jam’iyya tsakanin Chris Ngige da Andy Uba
  • Akwai yiwuwar wadannan rigingimu su yi tasiri wajen kawowa jam’iyyar APC cikas a zaben 2023

Matslolin da ake fama da su a jam’iyyar APC mai mulki nema suke yi su kara kamari, Daily Trust tace musamman a jihohin Gombe da kuma Anambra.

A jihar Gombe, tsohon gwamna watau Sanata Muhammad Danjuma Goje da magoya-bayansa suna rigima da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Sanata Muhammad Danjuma Goje ta bakin wasu lauyoyi da Barista Herbert Nwoye yake jagoranta, ya zargi gwamna mai-ci da sabawa Alkali.

Tsohon gwamnan yace gwamnatin Inuwa Yahaya ta shiga cikin batun da kotu tace a dakata tukun.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: APC ta sanar da ranar babban taron matan jam'iyya na ƙasa

Goje ya na tuhumar CJ da Kwamishina

Goje yana zargin kwamishinan shari’a, Zubairu Mohammed Umar da babban Alkalin jihar Gombe, Mu’azu Pindiga da cin zarafin wasu magoya-bayansa.

Daily Trust tace Sanatan na Gombe ta tsakiya ya na zargin wadannan mutane da fakewa da dokar kasa, wajen ganin bayan wadanda suke tare da shi.

Siyasar Gombe
Sanata Muhammad Danjuma Goje da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Rikicin Anambra ya na kara ci da wuta

A gefe guda, rigimar APC ta sauye zani a Anambra, inda Ministan kwadago na kasa, Chris Ngige yake rigima da Sanata Andy Uba wanda ya nemi gwamna.

Bangaren Sanata Chris Ngige sun dage a kan cewa ba Andy Uba ne jagoran jam’iyyar APC a Anambra, shi da mutanensa kuma sun ce babu wanda ya isa.

Hakan na zuwa ne bayan alkali mai shari’a, Inyang Ekwo ya ruguza zaben fitar da gwanin APC da ya ba Uba damar tsayawa takarar gwamna a zaben 2021.

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

Duk da hukuncin kotun ana cacar baki tsakanin mutanen Uba ta bakin Chukwunonso Chinwuba da bangaren Ngige, ta bakin na su kakakin, Okelo Madukaife.

Ana ganin irin wadannan sabani na cikin gida su na iya jawowa jam’iyyar APC matsala a zaben 2023.

Buba Galadima da kudirin zabe

A jiya aka ji Buba Galadima ya ce hasashen shi ya tabbata game da kudirin gyaran zabe. Galadima yace sai da yace a fille masa kai idan Buhari ya yarda da kudirin.

Buba Galadima ya ce idan aka sa hannu a dokar zabe, ko kujerar kansila APC ba za ta ci ba, ya kalubalanci Buhari, yace idan ya isa, ya sa hannu a kudirin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel