Sauya shekar kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP ba zai canza komai ba, Jam'iyyar AOC ta yi Martani

Sauya shekar kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP ba zai canza komai ba, Jam'iyyar AOC ta yi Martani

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ko a jikinta sauya shekar kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP be ɗaga mata hankali ɓa
  • Kungiyar dai ta fice daga APC kuma ta saɓar da komawa babbar jam'iyyar hamayya PDP a wani taro a Bukola Saraki ya halarta
  • APC tace tana fatan watarana kungiyar zata gano gaskiya kuma ta san cewa kullum.Legas kara cigaba take

Lagos - Jam'iyyar APC reshen jihar Legas, ta bayyana cewa rashin sa'a a jinin PDP yake, kuma dauya shekara kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP ba zai sauya komai ba.

The Cable ta rahoto cewa kungiyar wacce ke cikin APC, ta sauya sheka zuwa PDP ne ranar Asabar, a wurin wani taro da ya samu halartan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta lashe kujerun ciyamomi 35, Kansiloli 176 a zaɓen kananan hukumomin wannan jihar

Da yake martani a wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN), kakakin APC a Legas, Seye Oladejo, yace duk da haka ba abinda PDP zata iya yi a jihar Legas.

Bukola Saraki da Lagos4Lagos
Sauya shekar kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP ba zai canza komai ba, Jam'iyyar APC ta yi Martani Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Oladejo yace:

"Ba abinda zai faru ya baiwa jam'iyyar PDP nasara. A koda yaushe rashin nasara suke yi, domin a jininsu yake, saboda haka zasu cigaba da shan ƙasa ne."
"Ba wani cigaba da suke samu, mu haɗu a fagen fafata zaɓe, ina mai tabbatar muku ko gunduma ɗaya PDP ba ta iya lashewa a jihar nan."

Meyasa kungiyar ta sauya sheka?

Kakakin APC ya ƙara da cewa sauya shekar ƙungiyar ya bayyana butulcinsu ƙarara, kuma suna yaudarar kansu ne idan suna ganin zasu iya canza wani abu a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Yace tawagar yan Lagos4Lagos sun tabbatar da zaman su a tsagin adawa, kuma jam'iyya mai mulki ba ta ji komai ba kan ficewarsu.

"A koda yaushe suna ɓangaren adawa, mu muna ganin kamar shirin wasan kwaikwayo suke yi.
"Ba wanda zai zauna cikin jam'iyya mai mulki kuma ya rinka aiki irin na yan adawa. Saboda haka abu ne mai kyau da suka bayyana inda suka dosa."
"Muna fatan wataran zasu gane gaskiya kuma su san cewa a koda yaushe Legas gab take ƙara yi, sannan kanta a haɗe yake."

A wani labarin kuma tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace rikicin da ya baibaye jam'iyyar APC reshen Kano bai zo masa da mamaki ba.

Kwankwaso ya ɗora laifin akan gwamnan Kano na yanzu, Dakta Abdullahi Ganduje, inda yace halinsa na son kai ya jawo wannan rikicin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin gwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel