Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige

Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige

  • Hukumar zabe INEC tace har yanzun ba ta samu sahihin kwafin takardar hukuncin Kotu na tsige gwamna Umahi ba
  • Kwamishinan INEC na kasa ya ce da zaran sun samu takardar daga Kotu, za su kira zama domin nazari kanta
  • Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta kwace kujerar gwamna da kuma mataimakinsa na jihar Ebonyi kan sauya sheka

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC tace har yanzun ba ta samu kwafin takardar hukuncin da babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yanke kan Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa ba.

Festus Okoye, Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin tara bayanai, ne ya faɗi haka yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Abuja.

Premium Times ta rahoto Mista Okoye na cewa INEC zata zauna kan lamarin da zaran ta karbi takardar hukuncin da Kotu ta yanke.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

Shugaban INEC da gwamna Umahi
Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kwamishinan INEC ɗin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Har yanzun ba'a aiko mana da kwafin hukuncin da ake cewa Kotu ta yanke ba. INEC zata zauna ta yi nazari da zaran an miƙa mata takardar hukuncin Kotu ta gaske."

Ko wane hukunci Kotu ta yanke?

A ranar Talata, babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja karkashin jagorancin mai shari'a Inyang Ekwo, ta umarci gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya fice da ofis ɗin gwamna kan sauya shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

A hukuncin da Alkalin Kotun ya yanke, ya kuma umarci Mista Igwe da ya daina nuna kansa a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ebonyi.

Mai Shari'a Ekwo, ya bayyana cewa tun da sun fice daga PDP, jam'iyyar da mutane suka zabe su karkashinta, kama ta ya yi mutanen biyu su yi murabus daga kan mukamanssu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta amince da rahoton kwamitin tsarin mulkin karba-karba

Ya kuma ƙara da cewa saɓa wa doka ne ɗan takarar da aka zaɓe shi a wani muƙami karkashin jam'iyyar siyasa kuma ya koma wata jam'iyya ta daban.

Ya ce kuri'un da gwamna Umahi ya samu a zaben 9 ga watan Maris, 2019 na jam'iyyar PDP ne ba na APC ba.

A wani labarin kuma Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

Wasu kusoshin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Rano ta jihar Kano sun yi murabus daga kan mukamansu da nufin bin Kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai bar PDP kafin karshen watan Maris, alamu sun nuna zai koma NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel