Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin fitacciyar jaruma, Fati Washa

Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin fitacciyar jaruma, Fati Washa

- Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta san ta

- Jama’a sun fi sanin ta da Washa ko Fati Washa watau sunan Mahaifin ta ya bace.

Jarumar tana lokaci, tana samun aiki fiye da duk wata jaruma domin acikin fim biyar sai ka samu ta fito a uku ko hudu, daga cikin tsoffin finafinanta akwai Sarki.

Kadan daga cikin fina-finan wannan Jaruma akwai Ya Allah daga Allah, da tayi a 2014, 'Yar Tasha a 2015 Washa ta fito a Ana Wata ga Wata a shekarar 2015. Sannan ta fito a Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da sauransu.

Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin fitacciyar jaruma, Fati Washa
Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin fitacciyar jaruma, Fati Washa

KU KARANTA: Hotunan wata mata da ta haifi 'yan hudu a Katsina

Akwai jita-jita da take yawo akan Jarumar tana soyayya da Jarumi Adam A Zango, duk dai basu fito fili sun tabbatar ko karyata hakan ba, Amma kowa ya yadda fati washa tafi kowace jaruma kusa da Adam A Zango domin tun daga fim din Sarki har yanzu suna tare.

Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba suna rigima ko kuma jan fada.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng