"Ya Hadu": Wata Budurwa Ta Bar Wani Saurayi Ya Kwanta a Jikinta, Hotonsu Ya Ja Hankali

"Ya Hadu": Wata Budurwa Ta Bar Wani Saurayi Ya Kwanta a Jikinta, Hotonsu Ya Ja Hankali

  • Wata kyakkyawar budurwa ta haddasa cece-kuce a shafin Tuwita bayan ta saki hoton yadda wani ya kwanta a jikinta a Bas
  • Budurwar ta bayyana cewa abun ya bata sha'awa yadda mutumin bai tambayeta kuɗi ba kawai jingina ya yi da ita
  • Da yawan mutane sun mata rubdugun yabo kan yadda ta nuna soyayya ga wanda ba ta sani ba

Wata matashiyar budurwa a Najeriya, @Sweet_cocolatey ta bayyana wani Hoto wanda ya nuna haɗuwarta da wani Saurayin Fasinja a motar Bas ta haya.

A rubutun da ta saki a shafin Tuwita ranar Jumu'a, 2 ga watan Disamba, 2022, tace matashin saurayin ya ɗan huta a jikinta a lokacin da suke tsaka da tafiya a motar.

Matar da abun ya faru da ita.
"Ya Hadu": Wata Budurwa Ta Bar Wani Saurayi Ya Kwanta a Jikinta, Hotonsu Ya Ja Hankali Hoto: @sweet_cocolatey
Asali: Twitter

Ta yi dana sanin rashin karɓan lambarsa

Budurwar ta ƙara da cewa abinda mutumin ya yi ya ba ta sha'awa, inda ta nuna cewa ga dukkan alamu ya gaji ne sosai shiyasa ya ɗan kishingiɗa a kafadarta don ya ɗan huta.

Kara karanta wannan

Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Lambar Wani Mutumi a Gaban Matarsa, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Ja Hankali

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sweet Cocolatey ta ce ta yi dana sanin rashin neman lambar wayar mutumin. Ta rubuta cewa:

"Abun ya mun daɗi a rai na yadda ya kishingida a kafaɗata yana ɗan hutawa gunin sha'awa, bai nemo an taimaka masa da kuɗi ba. Kawai dai mutum ne da ya ɗan gaji ya jingina da ni, abun ya mun kyau."

Wasu da dama sun yi amfani da sashin faɗar ra'ayi inda suka fara rige-rigen ba da labarin yadda makamancin haka ta faru da su da waɗanda basu sani a Mota.

Martanin mutane a shafin budurwan

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a

@ladyvickie__ tace:

"Haka nima na ɗan kishingida a Motar wurin aikin mu na kwanta a jikin Oganmu, kar ku so ganin yadda ya hankaɗe ni ya share kafaɗarsa, na ji ba daɗi."

Kara karanta wannan

Kwana Huɗu da Aure, Amarya Ta Kama Ango Na Saduwa da Yar Uwarta a Gado, Ta Turo Bidiyo

@_molade__ yace:

"Wata rana wani zai zo yana faɗa mana yadda aka ci mutuncinsa. Na ji dadi baki kalli abun a haka ba ina fatan shi ma ba wata ɓoyayyar manufa ta sa ya yi ba."

@phthickgayguy yace:

"Muna godiyada yadda kika karbi yanayin, ƙasar nan ta ɗau zafi sosai, ɗan ƙaramin nuna kula ga mutanen da muka haɗu da su ka iya agaza musu a rayuwa."

A wani labarin kuma An nemi kai ruwa rana yayin da wata budurwa ta nemi wani bawan Allah ya ba ta lambarsa a gaban matarsa ta aure

A wani Bidiyon wasan barkwanci da mutane suka tofa albarkacin bakinsu, wata budurwa ta nuna ƙarfin halin tunkarar wani mutumi da tace ya haɗu sosai.

Dirarriyar budurwar ta nemi ya ba ta lambarsa ta waya duk da a gaban matarsa ne, abinda ya faru ya ja hankalin masu bibiyar bidiyon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel