An yi bikin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 601 a jihar Gombe

An yi bikin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 601 a jihar Gombe

Hedikwatar Tsaro ta kasa DHQ, ta sanar da cewa an yi bikin yaye tsofaffin 'yan Boko Haram 601 da suka tuba a jihar Gombe.

Tubabbun 'yan Boko Haram sun yi wa gwamnatin Najeriya rantsuwar ba zasu kara tsoma kansu a harkar kowane nau'i na ta'addanci ba.

Babban jami'in kula da Operation Safe Corridor, Bamidele Shafa, ya ce an yaye tubabbun 'yan Boko Haram din bayan an ba su kyakkyawan horo na gyara halayya da saisaita musu tunani da cire musu akidar ta'addanci a zukatansu.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, an yi bikin yaye tsoffin 'yan ta'addan ne a ranar asabar a sansanin zare akidar ta'addanci da gyara hali na Malam Sidi da ke karamar hukumar Kwami ta Jihar Gombe.

An yi bikin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 601 a jihar Gombe
Hoto daga jaridar The Cable
An yi bikin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 601 a jihar Gombe Hoto daga jaridar The Cable
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan kwanaki kadan da wasu mazauna jihar Borno suka nuna rashin amincewarsu da komawar tubabbun 'yan Boko Haram cikin al'umma domin ci gaba da rayuwa.

A shekarar 2016 ne rundunar dakarun tsaro ta Najeriya ta kaddamar da Operation Safe Corridor, wani shiri na gyara halin da saisaita tunani gami da zare akidar ta'addanci ga tsofaffin 'yan Boko Haram da suka tuba.

A cewar Bamidele, cikin tubabbun 'yan ta'addan da aka yaye akwai 14 'yan kasar Kamaru, Chadi da kuma Nijar.

A bangare guda kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, wani matashi mai shekaru 25 dan asalin jihar Kano mai suna Ashiru Musa Danrimi, ya kashe kansa ta hanyar sokawa cikinsa wuka a jihar.

An gano cewa matashin ya aikata hakan ne bayan budurwarsa da suka zuba soyayya za ta auri wani mutum na daban ba shi ba.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mamacin dan asalin gundumar Kadawa ne da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

Hankalinsa ya tashi kuma ya yi matukar harzuka bayan da ya gano cewa budurwasa mai suna Ummi Muhammad ta yanke hukuncin auran wani mutum da ba shi ba.

KARANTA KUMA: Hajj 2021: NAHCON za ta fara karbar kudin maniyyata a watan Satumba

Bincike ya nuna cewa, ya mayar da hankali ba kadan ba a kan soyayyarsu saboda ya sadaukar da kudinsa, aljihunsa da lokacinsa.

An zargi cewa ya soka wa kansa wuka bayan samun wannan labarin.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sanda jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce 'yan sanda sun gaggauta mika shi asibitin kwararru na Murtala da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Habu Sani, ya umarci sake bincike mai tsanani kuma gamsasshe a kan mummunan lamarin.

Makwabtan mamacin sun bayyana alhininsu da mamaki a kan aukuwar lamarin, domin kuwa sun san irin soyayyar da ke tsakanin masoyan. Basu taba tsammanin za ta kare a hakan ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel