"Gwara Na Je Gidan Yari"; Dangote Ya Fadi Abin da ba Zai Iya Rabu wa da Shi ba
- Hamshakin attajiri, Aliko Dangote ya ce zai fi son a tsare shi a gidan yari maimakon a hana shi amfani da wayarsa
- Attajirin ya bayyana cewa wayarsa na ɗauke da lambobin mutane sama da 13,000, waɗanda yake hulɗa da su a rayuwarsa da harkokin kasuwanci
- Dangote ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da shirin “Vision 2030”, wanda ya shafi bunƙasa masana’antu a Afirka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya ce zai fi masa sauƙi a tsare shi a gidan yari maimakon a ƙwace masa wayarsa.
Dangote ya bayyana hana shi amfani da wayar a matsayin abin da ba zai taɓa amincewa da shi ba.

Source: Getty Images
Dangote ya faɗi hakan ne a wani taro da aka gudanar a Legas, inda ya ƙaddamar da shirinsa na “Vision 2030” domin kawo sauyi a masana’antu a Afirka, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Dalilin da ya sa Dangote ba ya son a ƙwace masa waya
A yayin taron, an tambayi hamshaƙin ɗan kasuwar ko zai fi son ya shafe mako guda ba tare da wayarsa ba, ko kuma ya daina amfani da jirginsa na kashin kansa.
Da yake amsa tambayar, Dangote ya ce zai fi masa wahala ya rabu da wayarsa fiye da jirginsa na kashin kansa.
“Ah… Ina ganin ya fi sauƙi a saka ni a gidan yari maimakon a ƙwace mini waya. Don haka, ƙwace mini waya wani abu ne da ba zan amince da shi ba ko kaɗan,” in ji shi.
Dangote na da lambobin mutane sama da 13,000
Hamshaƙin ɗan kasuwar ya bayyana cewa wayarsa na ɗauke da lambobin mutane sama da 13,000, lamarin da ke nuna muhimmancin wayar wajen kula da yawan abokansa da abokan hulɗarsa na kasuwanci.
“Na san wannan zai zama kusan… Ina da wannan lambar tun lokacin… Twitter… Ina da lambobin mutane sama da 13,000 a wayata,” in ji Dangote.

Kara karanta wannan
Minista ya ɓallo ruwa a gaban ƙasashen duniya, ya yi maganar da ka iya juyo wa kan Tinubu
Da aka yi martani kan yawan lambobin da ke wayarsa, Dangote ya ce ba kasafai yake kulle lambobin mutane ba, kuma hakan na iya zama ɗaya daga cikin dalilan da suka sa adadin lambobin ya yi yawa.
“Ba kasafai nake kulle lambobin mutane ba. Ba na son kulle mutane, saboda haka akwai mutane da yawa,” in ji shi.
Yadda Dangote yake amfani da waya
Bayanin Dangote ya nuna yadda yake amfani da wayarsa wajen kula da hulɗoɗinsa na kai da na kasuwanci, duk da yawan ayyukan da yake jagoranta a sassa daban-daban na tattalin arziki a Afirka.
Harkokin kasuwancinsa sun haɗa da masana’antu, siminti, takin zamani, tace man fetur da sauran fannoni.
Dangote shi ne shugaban kamfanin Dangote Group kuma babban jami’in gudanarwarsa. Kamfanin na daga cikin manyan rukunonin masana’antu a Afirka.

Source: Facebook
Dangote ya dakatar da sayar da fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar mai ta Dangote ta dakatar da sayar da man fetur, ga manyan ’yan kasuwar da ke shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
Matatar ba za ta ƙara sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ke haɗa man Dangote da man da ake shigowa da shi ba.
Asali: Legit.ng
