Nazarin Shekara: Mutane biyar da suka tafka babbar asara a shekarar 2020

Nazarin Shekara: Mutane biyar da suka tafka babbar asara a shekarar 2020

- Rayuwa juyi-juyi; wai kwado ya fada ruwan zafi, in ji masu iya magana

- Ita dai duniya idonta a tsakar kanta ya ke, kuma duniya rawar 'yammata; na gaba ya kan koma baya idan an yi wani juyin

"A rayuwa wani lokacin kayi nasara wani lokacin kuma akasin haka,amma zaka cigaba da rayuwa" waɗannan sune kalaman da Adam's Oshiomhole ya yi bayan ya sha kayi a hannun ɗan cikinsa a siyasa, Godwin Obaseki, a wani nau'in kutufo amma fa irin na siyasa da Oshiomhole ya sha a zaɓen gwamnan jihar Edo na 19 ga watan Satumba.

A yayin da muke bankwana da shekarar 2020, Legit.ng ta yi nazari don kalato muku wasu fitattun ƴan siyasa a Najeriya da suka tafka gagarumar asara a lissafi irin na siyasa.

1. Adams Oshiomhole

Tsohon Shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole shine a farkon jadawalin mutanen. Baya ga asarar kujerar shugabancin jam'iyya mai mulki, Oshiomhole ya faɗi ƙasa wanwar a ƙoƙarinsa na sauke tsohon abokin siyasarsa, Godwin Obaseki, daga kujerar gwamnan jihar Edo.

2. Fasto Osagie Ize-Iyamu

Ize-Iyamu ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC wanda daga baya ya sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ya yi takarar gwamna a jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo a shekarar 2016.

KARANTA: Gayyatar Buhari: Majalisar dattijai ta juyawa majalisar wakilai baya

Sai dai karon bai masa daɗi ba bayan shan kayi da ya yi a hannun abokin karawarsa, Godwin Obaseki, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar APC kafin ya bar ta.

Nazarin Shekara:Mutane biyar da suka tafka tafkekiyar asara a shekaar 2020
Nazarin Shekara:Mutane biyar da suka tafka tafkekiyar asara a shekaar 2020
Source: Twitter

Sai dai a shekarar 2020, bayan juyin wainar siyasa, Ize-Iyamu ya samu takara a Jam'iyyar APC inda Obaseki ya zama ɗan takarar jam'iyyar PDP.

Abin baƙinciki shine duk da ƙarfin ikon da Oshiomhole ke da shi, hakan bai ceci APC daga sake shan kayi a hannun Obaseki ba.

KARANTA: Mu na son jin amsoshin tambayoyinmu guda uku daga bakin Buhari

3. Agboola Ajayi

A tsakanin watanni biyu kacal,Ajayi,mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC sai kuma daga ƙarshe zuwa Zenith Labour Party (ZLP).

Mataimakin gwamnan ya ɗimauce wajen son ya sauke mai gidansa, Rotimi Akeredolu, ya gaje kujerarsa a matsayin gwamna na gaba a jihar Ondo a zaɓen gwamnoni na ranar 10 ga watan Oktoba.

Bayan ya gaza samun tikitin takara a jam'iyyar PDP, sai ya tsallaka zuwa jam'iyyar ZLP inda ya zama ɗan takarar jam'iyyar.

Sai dai, duk da haka ya faɗi zaɓen domin kuwa bai zama gwani ba.

4. Babatunde Gbasamosi

Lokacin da ya bayyana a matsayin ɗan takarar jam'iyyar ADP (Action Democratic Party) yayin wata muhawarar ƴan takarar gwamna a shekarar 2019, mafi yawancin jama'a sun yaba da kaifin basirarsa da hankalinsa.

Abin baƙinciki, Gbadamosi ya kasa fassara nasarar muhawararsu zuwa nasara a akwatin zabe.

Ya faɗi zaɓen bayan ya sha kayi a hannun ɗan takarar jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu.

Bayan sauya sheƙarsa zuwa PDP don samun damar sake tsayawa takarar gwamna a jam'iyyar ADP, ana haka ya fara jagorantar jam'iyyar adawa.

Bayan ya faɗi takarar gwamna, ya sake tsayawa takarar Sanata a gabashin Legas a zaɓen ranar Asabar 5 ga watan Disamba. Sai dai, ba ta sauya zani ba, an sake kwatawa, ya sake shan kayi a hannun APC.

5. Chief Hillard Eta

Daga burinsa na son shugabantar APC, Eta ya ƙare a matsayin korarren dan jam'iyya mai mulki.

Kwamitin zartawa na APC (NEC) ya sanar da cewa jam'iyya ta ta kore shi.

Duk irin tsarinsa da lissafinsa na siyasa ta hanyar bayyana kansa a matsayin shugaban riƙon ƙwarya a APC bayan kotu ta bada umarnin dakatar Oshiomhole, yanzu Eta ya zama tarihi a jam'iyyar, har sai idan kotu ta soke hukuncin majalisar zartarwas na APC

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kwamitin shirye shirye da gudanarwar jam'iyyar APC ya sanar da ɗage shirinta na rijista da sake tantance ƴan jam'iyya wanda aka tsara gudanarwa ranar Asabar, 12 ga watan Disamba.

Yanzu za'a gudanar da rijistar a sati na biyu a cikin watan Junairun sabuwar shekara mai zuwa, 2021.

Sai dai jam'iyyar ta yi shiru akan takaimaimen kwanan watan da za'a gudanar da rijistar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel