Katsina: Hisbah ta Garkame Otal da Ya Saba Alkawari, Ana Zargin Badala da 'Yan Mata

Katsina: Hisbah ta Garkame Otal da Ya Saba Alkawari, Ana Zargin Badala da 'Yan Mata

  • Hukumar Hisba a jihar Katsina ta fusata kan yadda wani otal ya yi fatali da yarjejeniyar da gwamnatin jihar da sauran masu otal su ka sanyawa hannu domin kare kananan yara
  • Hukumar, ta bakin shugabanta Aminu Usman ta bayyana cewa ta rufe otal din New Palace ne saboda ba wannan ne karon farko da aka gano yara kanana sun kama daki a cikinsa ba
  • Sheikh Aminu Usman ya shaida cewa sai da su ka dade su na jan kunnen hukumomin otal din, amma sai ga shi an gano wasu yara mata kanana biyu sun kama daki yayin samamensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Bayan hana hawan Sallah, NSCDC ta dauki kwakkwaran mataki awanni kafin idi a Kano

Katsina - Hukumar hisba a jihar Katsina ta sanar da rufe wani otal bisa saɓa yarjejeniyar da su ka sanya hannu tsakanin dukkanin otal-otal ɗin jihar da hukumar.

Shugaban hukumar, Aminu Usman ne ya tabbatar da garƙame otal ɗin New Palace bayan zarginsa da bawa yara masu ƙarancin shekaru mafaka.

Katsina
Hukumar hisba ta rufe otal a Katsina Hoto: Legit ng
Asali: Original

The Cable ta wallafa cewa shugaban ya ce barin yara ƙanana su na zama a otal ya saɓa da dokar jihar Katsina da yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hisba ta gano yara a otal

Hukumar hisba a jihar Katsina ta bayyana cewa jami'an sintirinta sun gano wasu ƙananan yara mata biyu cikin ɗakin otal ɗaya, kamar yadda Sahara Reporters ta wallafa.

"Wannan shi ne karo na biyu da otal ɗin New Palace Hotel ke aikata wannan laifi duk da gargaɗinsu da mu ka yi a baya."

Kara karanta wannan

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta kama 'masu saida' takardar aiki a gwamnatin jiha

-Shugaban hukumar hisba, Aminu Usman.

A ranar 9 Yuni, 2024 ma'aikatar mata ta haramta barin yara masu ƙarancin shekaru su na zama a otal. Wannan ya biyo bayan ceto wasu yara mata 10 da aka yi safararsu daga Ghana.

Hisbah ta kama matasa a Kano

A wani labarin kun ji cewa hukumar hisbah ta jihar Kano ta kara tsaurara matakin kauda badala bayan ta cafke wasu matasa maza da mata 20 su na ninkaya tare a gidan shakatawa.

Hukumar ta bayyana cewa an yi kamen ne bayan sun samu korafi daga al'umar yankin titin ring road inda su ka ce matasan sun dame su kuma su na gurbata masu unguwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.