Jihohin Najeriya: Inda Aka Fi Yawan Kiran Waya da Amfani Da ‘Data’ a Kasar Nan

Jihohin Najeriya: Inda Aka Fi Yawan Kiran Waya da Amfani Da ‘Data’ a Kasar Nan

  • Ofishin kididdiga a Najeriya na NBS ya fitar da rahoton sadarwa da amfani da kayayyakin fasaha a kasar
  • An bayyana adadin amfani da wayoyin hannu da aka yi; kama daga kira har zuwa amfani da shafukan sada zumunta
  • Hakazalika, an bayyana jihohin da suka fi yawan amfani da wadannan kayayyaki na fasaha da kuma layin da aka fi amfani dashi

Najeriya - Legas, Ogun da Kano ne jihohin da suka fi yawan masu amfani da wayoyin hannu da kuma hawa shafukan intanet, inji ofishin kididdiga na NBS, inji rahoton Business Day.

A rahoton da NBS ya fitar na harkokin tarho, ya kunshi bayanai game da amfani da wayoyi ‘data’ a watanni uku na karshen 2022.

Hakazalika, bayanan sun kunshe adadin masu kiraye-kirayen waya, amfani da shafukan intanet har ma da kamfanonin sadarwar da ‘yan Najeriya ke amfani dasu.

Kara karanta wannan

Masha Allah An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan, Yau Za a Kwaso Da Dama

Inda aka fi amfani da wayoyin hannu da 'data'
Wayar hannu ta Android da ake amfani da ita a Najeriya da wasu kasashen duniya | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Kididdigar da NBS ya fitar; inda aka fi kira da amfani da ‘data’

Rahoton na NBS ya bayyana cewa, a karshen watanni ukun 2022, ‘yan kasar nan sun yi kiran waya sau 222,571,568. Yawan wadanda suka yi amfani da intanet kuma ya kai 154,847,901.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

1. Jihar Legas

Kiran waya: 26,460,867

Amfani da ‘data’: 18,702,394

2. Jihar Ogun

Kiran waya: 12,994,352

Amfani da ‘data’: 9,206,614

3. Jihar Kano

Kiran waya: 12,373,201

Amfani da ‘data’: 8,470,131

Kididdigar da NBS ya fitar; inda aka suke a kuran baya a kira da amfani da ‘data’

1. Jihar Ekiti

Kiran waya: 2,001,846

Amfani da ‘data’: 1,474,970

2. Jihar Ebonyi

Kiran waya: 1,920,996

Amfani da ‘data’: 1,264,825

3. Jihar Anambra

Kiran waya: 1,571,692

Amfani da ‘data’: 1,101,002

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: An Gano Wanda Tsofaffin ‘Yan Majalisar Tarayya Suke Goyon Baya a APC

Kamfanin sadarwa na MTN aka fi amfani dashi a Najeriya, inda aka yi kiran da ya kai 89,016,678 da kuma amfani da ‘data’ da ya kai 65,619,610, NairaMetrics ta tattaro.

Alkawura 3 da Buhari ya yi, amma ya gaza cikawa

A wani labarin kuma, mun tattaro muku wasu manyan alkawuran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yiwa ‘yan kasa amma ya gaza cikawa.

A rahoton, an kawo tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa a matsayin abubuwan da Buhari bai tabuka abin da ya kamata da ake tsammani ba.

Sai dai, an yaba wa shugaban kasan wajen cimma nasara a fannin gine-gine da samar da ababen more rayuwa a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel