Da dumi dumi: Buhari ya sabunta lasisin mallakar rijiyoyin mai guda 25

Da dumi dumi: Buhari ya sabunta lasisin mallakar rijiyoyin mai guda 25

Gwamnatin tarayya ta sabunta ma kamfanonin yan kasuwa dake hakar man fetir lasisin da zai basu damar cigaba da mallakar rijiyoyin mai guda ashirin da biyar a Najeryia, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin tarayya ta hukumar kula da albarkatun man fetir, DPR, ta bada uamrnin bude sabbin rjiyoyin mai guda goma sha shida domin kara yawan adadin gangar danye man da Najeriya ke fitarwa da ganga dubu dari biyar da sitti, da Arba’in da sittin da uku, 560,463.

KU KARANTA: Ana tuhumar wani Sanatan jam’iyyar PDP da amfani da takardun karatu na bogi

Da dumi dumi: Buhari ya sabunta lasisin mallakar rijiyoyin mai guda 25

Rijiyar Mai

Da wannan sabunta lasisi 25 da gwamnatin Buhari ta yi, za ta samu kudi dalan Amurka biliyan daya, kimanin naira biliyan dari uku da hamsin kenan, hakan zai taimaka mata wajen gudanar da kasafin kudin bana.

Daga cikin wadanda suka amfana da wannan sabuntawa akwai kamfanonin kasashen waje da na yan Najeriya, inda suka biya kudin neman sabuntawa na dalan Amurka miliyan biyu, kimanin naira miliyan dari bakwai kenan, kowannensu.

A wani labari makamancin wannan, DPR ta sanar da bada sabbin lasisi goma ga kamfanoni daban daban da suke da burin habbaka sarrafa iskar gas tare da kafa kamfanin sarrafa taki a Najeriya, daga karshe hukumar tace ta tara ma gwamnati adadin kudi N747,614,888,823.04 a shekarar 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel