Ajali Ya Gitta: Shugaban Hukumar BASHCMA da 'Ya'yasa 4 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

Ajali Ya Gitta: Shugaban Hukumar BASHCMA da 'Ya'yasa 4 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Alhaji Ibrahim Ladan Duguri, shugaban hukumar kula da tsarin inshorar lafiya ta jihar Bauchi, ya rasu tare da ’ya’yansa huɗu a hatsarin mota
  • Gwamna Bala Mohammed ya bayyana alhini kan rasuwarsa, inda ya ce babban rashi ne ga jihar Bauchi, musamman ɓangaren lafiya
  • Za a gudanar da sallar jana’izar mamatan a fadar Dagacin Yalwan Duguri da ƙarfe 11:00 na safe ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Alhaji Ibrahim Ladan Duguri, shugaban hukumar kula da tsarin inshorar lafiya ta jihar Bauchi (BASHCMA), tare da ’ya’yansa huɗu sun rasu a wani hatsarin mota da ya faru a Yalwan Duguri, ƙaramar hukumar Alkaleri.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan wannan rashi.

Alhaji Ibrahim Ladan Duguri.
Shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Ladan Duguri Hoto: Abdulaziz Duguri
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, gwamnan ya bayyana rasuwar Alhaji Ibrahim Ladan Duguri a matsayin babban rashi ga jihar Bauchi, musamman fannin lafiya.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: An tsinci gawar magidanci da wani irin rauni a al'aurarsa, matarsa ta gudu

Gwamna Bala ya yi ta'aziyya

Ya ce marigayin ya yi fice wajen jajircewa, sadaukarwa da kuma himma wajen inganta damar samun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.

A cikin saƙon ta’aziyyarsa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya kuma nuna alhininsa kan yadda hatsarin ya faru.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, majalisar masarautar Duguri, abokansa, abokan aikinsa da kuma daukacin al’ummar jihar Bauchi bisa wannan babban rashi.

Haka kuma, gwamnan ya yi addu’ar samun cikakkiyar lafiya, ƙarfi da kwanciyar hankali ga Suleiman, ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayin da aka ruwaito ya tsira daga hatsarin.

Gudummawar marigayin a fannin lafiya

Gwamna Bala Mohammed ya ce:

“A matsayinsa na shugaban BASHCMA, marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tsarin kula da inshorar lafiya a da kuma tallafa wa ƙoƙarin samar da sauƙin samun kiwon lafiya ga al’umma, musamman masu ƙaramin ƙarfi.

Kara karanta wannan

Oyebanji ya kafa tarihi da aka rantsar da shi a matsayin gwamna karo na 2 a Najeriya

“An kuma ga jajircewarsa ta hanyar gudummawar da ya bayar ga tawagar likitocin jihar Bauchi a lokacin ayyukan aikin hajji a Masarautar Saudiyya, inda aka yaba da ƙoƙarinsa wajen kula da lafiya da walwalar mahajjata.
“Baya ga nasarorin da ya samu a aikinsa, Alhaji Ibrahim Ladan Duguri babban abokina ne na kut da kut, kuma mun yi karatu tare.

Gwamnan ya bayyana cewa babu kalmomin da za su iya bayyana irin zafin da iyalan mamatan ke ciki a wannan lokaci mai wuya.

Ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki, cikin rahamarsa marar iyaka, ya gafarta wa mamatan kurakuransu, ya karɓi kyawawan ayyukansu, ya kuma ba Alhaji Ibrahim Ladan Duguri da ’ya’yansa masauki a Aljannatul Firdaus.

Za a gudanar da sallar jana’izar mamatan a fadar Dagacin Yalwan Duguri da ƙarfe 11:00 na safe ranar Lahadi.

Kun ji cewa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ya rasa mai magana da yawunta, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Saminu ya yi fice musamman wajen samar da bayanai cikin lokaci kan gobara, matakan kariya, ayyukan ba da agajin gaggawa da sauran ayyukan da suka shafi kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262