Yadda Aka Sace Mahaifiyar Tsohuwar Minista Bayan Tonon Silili Kan Kudin Tallafi
- Tsohuwar minista a Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa dalilin sace mahaifiyarta a shekarar 2012 bayan bincikenta
- Okonjo-Iweala ta ce masu garkuwa da mahaifiyarta sun buƙaci ta yi murabus daga mukaminta tare da barin ƙasar
- Tsohuwar ministar ta ce mahaifiyarta ta shafe kwanaki biyar a hannun masu garkuwa da mutane a daji, kafin ta tsere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohuwar minista a Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta yi magana kan yadda aka yi garkuwa ta mahaifiyarta.
Shugabar Hukumar Ciniki ta Duniya (WTO), ta ce binciken da ta gudanar kan zargin almundahanar dala biliyan 2.4 a tallafin man fetur ya jawo sace mahaifiyarta.

Source: Getty Images
A wata hira da ta yi da Bloomberg da TheCable ta bibiya, Okonjo-Iweala ta ce masu garkuwa da mahaifiyarta sun buƙaci ta yi murabus daga mukaminta na ministar kuɗi tare da barin Najeriya.
Yaushe Ngozi ta rike mukamin minista?
An yi garkuwa da Kamene Okonjo, mahaifiyarta, daga gidanta da ke Ogwashi-Uku, jihar Delta, a watan Disambar 2012.
Okonjo-Iweala ta riƙe muƙamin ministar kuɗin Najeriya daga shekarar 2011 zuwa 2015, a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Ta ce binciken tallafin man fetur ya fara ne bayan ofishinta ya lura da wani gagarumin ƙaruwa a ikirarin kuɗaɗen da masu shigo da fetur ke gabatarwa domin a biya su.
Ta ce:
“Sai na je wurin shugaban ƙasa na ce masa, ga shi nan, akwai wani abu da ke faruwa. Za mu iya bincikar asusun kuɗaɗen? Ya ce, eh, a ci gaba. Sai muka gano almundahana ta kusan dala biliyan 2.4. Saboda haka, muka ƙi biyan kuɗin.”
Ta ce an sace mahaifiyarta jim kaɗan bayan sanar da matakin ƙin biyan kuɗin, inda ta ƙara da cewa masu garkuwar sun buƙaci ta yi murabus a matsayin sharadin sakin mahaifiyarta.
Ta ce:
“An gaya mini cewa domin a saki mahaifiyata, dole ne in yi murabus kuma in bar ƙasar.”

Source: UGC
Abin da ya fi tayar mata da hankali
Tsohuwar ministar ta bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tayar mata da hankali a rayuwarta, tana mai cewa an tsare mahaifiyarta a cikin daji kafin ta samu damar tserewa.
Okonjo-Iweala ta ce:
“An tsare ta a tsakiyar wani daji, kuma wata dare ta tsere. Har yanzu tana raye. Yanzu tana da shekaru 96.
“Kwanaki biyar ne masu matuƙar muni. Ina ganin wannan ne mafi muni a rayuwata.”
Okonjo-Iweala ta ce ta yi tunanin yin murabus kafin a saki mahaifiyarta, amma mahaifinta ya gargaɗe ta kan kada ta amince da buƙatun masu garkuwar, cewar Punch.
Gwamnati ta fadi ribar cire tallafin mai
An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ce ta samu dala miliyan 500 ba tare da karɓar bashi ba domin sake gina filin jirgin sama na Legas.

Kara karanta wannan
Dalla dalla: Yadda za ka duba wayarka ta cika sharaɗin NCC domin kada a rufe maka ita
Festus Keyamo ya danganta ƙarin kuɗaɗen da aka samu da ajiyar kuɗin waje da sauye-sauyen tattalin arziki bayan cire tallafin man fetur.
Ministan ya ce ƙarin masu zuba jari daga kasashen waje zai taimaka wajen samar da kuɗaɗe, ababen more rayuwa da guraben aikin yi ga ’yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

