Yanzu Yanzu: Amurka ta goyi bayan Okonjo-Iweala ta jagoranci WTO
- Kasar Amurka ta goyi bayan Okonjo-Iweala domin aikin Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO)
- Ku tuna cewa tsohuwar gwamnatin Trump ta ki mara mata baya saboda wasu dalilai
- Yan Amurka sun jinjina mata kan kasancewa da tarin sani a fannin tattalin arziki da diflomasiyyar kasa da kasa
Duk da cewar gwamnatin Shugaba Trump ta ki lamuncewa takarar Ngozi Okonjo-Iweala don jagorantar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), tsohuwar ministar kudin ta Najeriya ta samu muradinta.
Musamman, gwamnatin Joe Biden a ranar Juma’a, 5 ga watan Janairu, ta bayar da cikakken goyon bayanta a kudin Okonjo-Iweala.
KU KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya da manoma: Tinubu ya yi shiru ne saboda baya so ya rasa hulunansa, Sani
Ku tuna cewa Trump ya ki amincewa da ita duk da goyon bayan da ta samu da sauran kasashe da dama.
KU KARANTA KUMA: Ba za mu bari mutum 1 ya jawo mana rikici ba, Ganduje ya bayyana dalilin haramta wa Sheikh Kabara yin wa’azi
A cewar wakilan kasuwanci na Amurka, tana da tarin ilimi a fannin tattalin arziki da diflomasiyyar kasa da kasa.
Bugu da kari, yan Amurkan sun yaba mata a kan “nuna kwarewa wajen kula da babban kungiyar kasa da kasa.”
A baya mun ji cewa wasu shugabanni a Amurka har da Joseph Stiglitz, sun aika wasika ga Joe Biden, suna rokon shi ya goyi bayan takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a kungiyar WTO.
A wata budaddiyar wasika da manyan suka rubuta wa sabon shugaban kasar, sun ba Jode Biden shawarar cewa za a yaba idan ya ba Ngozi Okonjo-Iweala goyon baya.
Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, ana ganin cewa Duniya za ta yi wa Biden kallon ya na jawo kowa a jika idan ya goyi bayan tsohuwar Ministar Najeriyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng