Bincike: Akwai bindigogi AK-47 sama da 60,000 a sansanonin 'yan bindiga 120
- Wani malamin jami'a ya gudanar bincike, inda ya gano wasu abubuwan ban tsoro game da 'yan bindiga
- A cewarsa, ya gano a kalla akwai bindigogi AK-47 60,000 a sansanonin 'yan bindiga sama da 120 a yankin Arewa maso yamma
- Ya kuma ba da wasu alkaluman kashe-kashe da barnar 'yan bindiga a dukkan yankunan na Arewa maso yamma
Sokoto - A wani rahoto da muka sami, an ce akwai akalla sansanonin 'yan ta'adda 120 da ke da mallakin bindigogi kirar AK-47 guda dubu 60, a Jihohin Arewacin kasar nan shida, Tribune Nigeria ta ruwaito.
Jihohin sune Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna, Kebbi da Neja kuma kowanne daga cikin kungiyoyin ta’addancin 120 sun mallaki bindigogi AK-47 sama da 500.
Wadannan bayanan suna kunshe ne cikin binciken shekaru goma da wani babban malami a Sashen Tarihi na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Dakta Murtala A. Rufa’i ya gudanar.
Malamin, wanda ya bi diddigin ayyukan ta’addanci daga shekarar 2011, ya kuma ce sama da rayuka 12,000 ne suka salwanta a ta’addanci a jihar Zamfara kadai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma bayyana cewa kimanin dabbobi 250,000 aka sace, yayin da aka lalata kauyuka 120 sannan sama da mazauna kauyuka 50,000 da 'yan ta'adda suka raba da muhallansu a cikin wannan lokaci da ya yi nazari.
Ya yi wannan jawabi ne a wata laccar jami'ar a zaman wani bangare na shirye-shiryen karawa juna sani kan fashi da makami a shiyyar Arewa maso Yamma.
Yayin da yake gabatar da takardar binciken mai taken, “Ni Dan Bindiga ne: Shekaru Goma na Bincike a Maboyar 'Yan Ta'adda a Zamfara”, Rufa’i ya ce ya yi mu’amala daya bayan daya da wasu shugabannin kungiyoyin ta’addanci.
A cewarsa, wadannan gungun 'yan bindiga da gaske suna kisan gilla kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, satar shanu, garkuwa da mutane, cin zarafin mata da sauran laifukan da suka danganci take hakkin dan adam.
A cewarsa:
“Da farko, sun zauna a cikin dazuzzuka da duwatsu inda suke kaddamar da ta’addanci a yankunan karkara da birane na jihohi. Amma wasu daga cikin 'yan bindigar sun zama masu karfin hali har suke iya farautar su daga garuruwan su."
Ya kara da cewa:
“Sansanoni masu karfi da kungiyoyi kamar wanda Dan-Karami na Zurmi ke jagoranta, Alhaji Auta na Birnin Magaji, Halilu na Chafe, Turji na Isa da Dogo Gide na Birnin Gwari suna da karfin kudi da hadin gwiwa don siyan adadi mai yawa. na makamai.”
Rufa’i ya bayyana a cikin bincikensa na karawa juna sani, inda ya yi cikakken bayani kan yadda 'yan bindigan suke sake shiga cikin kungiyoyin ta’addanci.
'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wadanda suka kashe Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, inji rahoton jaridar Punch.
An kashe dattijon dan shekara 93 bayan da masu garkuwa da mutanen suka sace shi suka kuma karbi kudin fansa miliyan 10 daga iyalansa.
Jagoran gungun masu garkuwa da mutane, Jethro Nguyen, dan shekara 53, ya ce ya dauki hayar wasu mutane 10 ciki har da wasu Fulani makiyaya don sace tsohon a gidansa, ya kara da cewa sun tsare shi a maboyarsu na kusan kwanaki 10 kafin su hallaka shi.
Ya ce sun yi garkuwa da mamacin ne saboda za su iya samun kudi cikin sauki daga gareshi kasancewar dansa ya taba yin gwamna a jihar Filato, kuma sanata a Najeriya.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina
A wani labarin, 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.
Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar.
Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba. Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.
Asali: Legit.ng