Manyan Dalilai 7 Masu Hadari Zai Sa Kowa Ya Guji Cin Gandar Fatan Dabbobi
Yarbawa na kiransa 'Ponmo', Inyamurai kuma 'Kanda', Hausawa kuwa na cewa 'Ganda', fatar dabbobi na daga cikin abincin da 'yan Najeriya ke ci ba kakkautawa.
Gwamnati ta ce sam bai kamata jama'a suke cin wannan nau'in naman ba saboda yana rusa masana'antun fatu a kasar.
A 2019, hukumar kula da abinci da magunguna NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya game da cin ganda, inda tace yana da matsala ga lafiya.
Daraktan NAFDAC, Moji Adeyeye ya ce, bincike ya nuna 'yan kasuwa na siyar da fatun da ya kamata ace na masana'antu ne zuwa abincin da ake ci.
Although, different health experts have argued for and against the nutritional value of Ponmo, it has not stopped those who love it (Ponmo) to stop consuming it. In fact, it has become a daily staple delicacy for consumption.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk da gargadin illa ga lafiya da kuma durkusar da masanatun fata, har yanzu ganda na daga cikin abincin 'yan Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A kasa mun kawo muku jerin illolin cin ganda
1. Da yawan fatun dabbobi ana samar dasu ne don amfanuwar masana'atun fatu, amma ake samunsu a tukwanen jama'a. Don haka, akwai illa ga lafiyar dan adam a cinsa.
2. Wasu daga cikin fatun da ake kawo wa kasuwa suna dauke da sinadaran ajiya masu illa, wadanda ka iya cutar da jikin dan adam.
3. Wasu fatun da ake kawowa daga kasashen waje ba na ci bane, ana kawowa ne domin aiki dasu a masarrafar takala da jaka da sauransu, ba shakka hakan matsala ne ga lafiya.
4. Fatun da ake kawowa daga kasashen waje sun fi araha saboda illarsu, kuma basu da tsaftar da fatun da ake samu a gida Najeriya. Wannan yasa 'yan kasuwa ke kawowa don riba, 'yan Najeriya kuwa ke ci cikin rashin sani duk da illolinsa.
5. Ya kamata masu kiwon dabbobi su sani cewa, fatun da ake kawowa don masana'antu ba na amfani bane a sarrafa abincin dabbobi. Amfani dasu kuwa matsala ce ga lafiyar jama'a.
6. Akwai yiwuwar samun matsalar hanta, koda da bugun zuciya ta dalilin ganda, ga kuma wasu karin cututtuka dake tattare da cinsa.
7. Yadda ake sarrafa fatu na daya daga cikin hanyoyi mara natuswa, don haka akwai yiwuwar samun barazanar lafiya daga cin irin wadannan fatun.
Jaridar Punch a 2019 ta taba wallafa illolin cin ganda makantan wadannan.
Akwai rashin fahimta
Bayan ganin yaawaitar cece-kuce daga bangarori daban-daban na Najeriya kan yunkurin gwamnati na hana cin fatun dabbobi, mun tattauna da wata mai sani game da abinci da kuma lafiyar jikin dan adam.
A tattaunawar wakilin Legit.ng Hausa da malamar jami'ar jiha ta Gombe, Zainab Abubakar Aliyu, ta ce akwai rashin fahimta kan yadda ake ririta batun haramta cin ganda.
Ta ce:
"Ba wai bayani ne na hani kan cin gandan shanu ba, batu na na duba lafiya. Wasu na kafa hujjan taba na da illa ba a hana ba, wannan wani magana ne daban.
"Gandan nan ba wani fa'ida yake dashi ba, amma bana ganin hana shi ne mafita. Tabbas wanda ake saka masa sinadarai zai zama da matsala, irinsu fomalin da dai sauransu idan bai samu dahuwa mai kyau ba.
"To ka ga daga cin abinci mai kyau, ka samu matsala. Yakamata ana duba mai kyau a kasuwa. Shawari na shine mutum ya tafi wurin masu yanka shanu, zai samu mai kyau da aka kona a ranan.
"Amma wanda aka adana ya dade, gaskiya akwai alaman yana da sinadarai masu hatsari ga lafiyan mutum.
"Bana tunanin wannan zai zama matsala, kawai dai a bar wanda aka adana saboda masu jiman fata, su kuma masu ci su nemi wanda bai dade ba."
Gwamnatun Najeriya Ta Ce Cin Fatan Dabbobi Bai da Wani Amfani, Za a Haramtawa ’Yan Najeriya
A wani labarin, gwamnatin Najeriya na shirin kawo kudirin dokar da zai haramta cin fatar dabbobi da aka fi sani Ponmo a kasar saboda habaka masana'antun fata.
Muhammad Yakubu, babban daraktan cibiyar fata da kimiyya ta NILEST dake Zaria ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, TheCable ta ruwaito.
Yakubu ya ce wannan yunkuri ya zama dole domin farfaɗo da masana'antun fata a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng