Yanzu-yanzu: Za a hana sallar Juma'a da taron coci na ranar Lahadi a Legas saboda Coronavirus

Yanzu-yanzu: Za a hana sallar Juma'a da taron coci na ranar Lahadi a Legas saboda Coronavirus

Gwamnatin jihar Legas ta ce za ta bukaci shugabannin musulmi da na kirista a jihar su dakatar da yin sallar Juma'a a masallatai da kuma taron ibadah na ranar Lahadi a coci a jihar domin kare yiwuwar yaduwar coronavirus.

Kwamishinan labarai na jihar, Mista Gbenga Omotosha ne ya bayar da wannan sanarwar yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Laraba jim kadan bayan an tabbatar da sabin mutane biyar na dauke da kwayar cutar a jihar.

Yanzu-yanzu: Za a hana sallar Juma'a da taron coci na ranar Lahadi a Legas saboda Coronavirus
Yanzu-yanzu: Za a hana sallar Juma'a da taron coci na ranar Lahadi a Legas saboda Coronavirus
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Ya ce, "Mun san cewa gwamnatin tarayya ta umurci hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta rufe sansanoninta. A ranar Talata, kwamishinan harkokin cikin gida ya ce za a gudanar da taro da shugabannin addinai.

"Za mu ba su shawarar cewa a dakatar da yin sallar Juma'a da ibadah na ranar Lahadi a duk wurin da mutane da yawa ke taruwa.

"Duba da yadda lamara ke tafiya a yanzu, ina da tabbacin cewa za a basu shawarar su dakatar da yin ibadan cikin taron mutane domin kiyaye lafiyar mu baki daya. Ina da tabbacin za su amince da hakan."

A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnonin yankin Arewa maso yamma sun sanar da cewa za a rufe dukkan makarantu da ke yankin na tsawon kwanaki 30 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cikin sakon bayan taro da gwamnonin suka fitar ta bakin shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, sun ce ya zama dole a dauki matakin hakan domin kare yaduwar cutar da Coronavirus a yankin.

An samu samu bullar wata cuta da ake zargin coronavirus ne a jihar ta Katsina a karo na farko a ranar Laraba.

Gwamanonin sun yi taro na a Kaduna domin bita kan kallubalen tsaro da ke adabar yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164