Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa

Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa

  • A karshe ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi murabus daga matsayinsa a majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Amaechi ya sauka daga mukaminsa ne domin ya mayar da hankali ga kudirinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • A bangaren ministan shari'a Abubakar Malami, har yanzu bai mika takardar ajiye aiki ba duk da cikar wa'adin da Buhari ya bayar a yau

Ministan sufuri kuma mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Rotimi Amaechi, ya yi murabus daga kujerarsa.

Wannan mataki da ministan ya dauka ya yi daidai da umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa yan majalisarsa da ke da aniyar tsayawa takarar wata kujera a zabe mai zuwa, Sahara Reporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa
Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa Hoto: Deedaddy Abdullahi
Asali: Facebook

An tattaro cewa Amaechi ya ajiye aikin minista ne a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, wanda ya yi daidai da cikar wa’adin da shugaban kasar ya bayar.

Sai dai kuma, ministan shari’a kuma Atoni janar na kasar, Abubakar Malami, ya ki yin murabus duk da cewar yau Litinin ne karshen wa’adin da shugaban kasar ya bayar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malami dai ya ayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar gwamnan jihar Kebbi a watan Afrilu.

Sahara Reporters ta kuma rahoto daga wasu majiyoyi cewa a ranar Juma’a da ta gabata, Malami ya janye daga tseren gwamnan jihar Kebbi.

Ya raba manyan motoci fiye da 200 ga mambobin jam’iyyar gabannin zaben fidda gwani na gwamna a jihar.

Ya kuma gabatar da fom din jam’iyyar na naira miliyan 50 a cibiyar taro ta kasa da kasa.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Majiyoyi da dama na kusa da ministan sun bayyana cewa ya janye daga tseren ne kan tsoron cewa ba lallai ne ya mallaki tikitin ba.

Ministar Buhari ta lashe amanta, ta janye daga takarar kujerar sanata

A gefe guda, ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta janye daga kudirinta na takarar kujerar sanata a babban zaben 2023 mai zuwa.

Tallen wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, ta kuma ce bata yi murabus daga matsayinta na minista ba, Daily Trust ta rahoto.

Ta bayyana cewa ta yanke hukuncin ne domin ta samu damar mayar da hankali kan tubalin da aka gina wajen ci gaba da tabbatar da daidaiton jinsi a mukaman shugabancin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel