Mai Digiri ya koma sayar da shayi

Mai Digiri ya koma sayar da shayi

– Aliyu Ahmed Kabir ya kammala karatun san a Digiri, amma ya koma harkar shayi da biredi

– Yanzu haka da wannan sana’a yake cin abinci

– Aliyu na zaune a Garin Kafanchan a Jihar Kaduna, yace Takardar karatu ba ta hana nema

Mai Digiri ya koma sayar da shayi
Mai Digiri ya koma sayar da shayi

Wani Bawan Allah mai suna Aliyu Ahmed Kabir ya dage da sana’ar sayar da shayi da Biredi bayan ya kuwa kammala karatun sa na Jami’a. Yanzu haka Aliyu yana da Dan Teburin sa na shayi a kan layin Bebeji da ke Kafanchan a cikin Kudancin Kaduna.

Aliyu ya karanta Ilmin ma’adanai na karkashin kasa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta Bauchi tun a shekarar 2013. Kafin nan ma Aliyu ya karanci abin da ya shafi kiwon lafiya a wata Makarantar tsabta ta Jihar da ke Ningi.

KU KARANTA: An kai hari a Madagali

Aliyu dai yace in dai shayi ne, gado yayi. Kuma halin rashin aikin yi a Kasar ya sa ya cigaba da wannan sana’a. Daridar Daily Trust tace Aliyu ya bayyana cewa ya kan yi dariya idan har ya ga masu karatun diploma da shaidar NCE suna yanga wajen neman aiki, Aliyu yace takardar shaida ba karan komai bace.

Idan ba a manta ba wancan makon, Malaman Makaranta da dama sun koma azumi inda suke rokon Ubangiji ko a samu a biya su albashin sun a wata-da-watanni. Ma’aikatan Makaranta na bin Gwamnatin Jihar Kwara dai bashin albashi har na watanni 6. Sai dai da alamu an kuwa karbi addu’ar su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel