An Kame Dan Sandan Bogi da Ake Kitsa Kone-konen Ofisoshin 'Yan Sanda Dashi

An Kame Dan Sandan Bogi da Ake Kitsa Kone-konen Ofisoshin 'Yan Sanda Dashi

- Rundunar 'yan sanda ta jihar Imo ta yi nasarar kame wani dan bindiga mai ikrarin cewa shi dan sanda ne

- An kama shi da bindiga da tarin harsasai da kuma kakin 'yan sanda a cikin wata motar da aka kame shi a ciki

- Rundunar ta bayyana cewa, tana bincike kan lamarin yayin da take neman hadin kan al'ummar jihar

A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta ba da sanarwar cewa ta cafke wani dan sanda na bogi kuma dan bindiga, mai suna Michael Osundu.

A cewar kakakin rundunar, tare da Orlando Ikeokwu, an gano bindiga guda daya da harsasai 26, da kuma kakin ‘yan sanda guda biyu masu mukamin Mataimakin Sufeta Janar, wadanda aka boye su a cikin motarsa ​​kirar Toyota Escalade mai bakin gilashi.

Ikeokwu ya bayyana cewa ana zargin Osundu dan kungiyar 'yan daba ne da suka kai hari hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar da kuma gidan yari na Owerri a ranar 5 ga Afrilu, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: NLC: Tuni El-Rufai Ya Koma Biyan N18,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi

An Kame Dan Sandan Boge da ke Kitsa Kone-konen Ofisoshin 'Yan Sanda
An Kame Dan Sandan Boge da ke Kitsa Kone-konen Ofisoshin 'Yan Sanda Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kakakin ‘yan sandan ya ce, "Jami'an rundunar, yayin da suke gudanar da sintiri tare da karfafa gwiwa, sun kama wani Michael Osundu na Owerri, wanda ya yi ikirarin cewa yana zaune a Landan.

“An kama shi ne tare da aikata laifuka a cikin jihar kuma ana tsammanin yana daga cikin 'yan bindigan da suka kai hari ga Ofishin Gidan Yari na Najeriya da hedkwatar ‘yan sanda a ranar 5 ga Afrilu.

“Haka nan, a daidai lokacin da aka kama shi, an gano bindiga guda daya da harsasai 26, da kuma kakin 'yan sanda guda biyu masu mukamin Mataimakin Sufeta Janar na ‘Yan Sanda da ya boye a cikin motarsa ​​kirar Toyota Escalade.

“Bayan bincike, ya yi ikirarin cewa shi dan leken asirin 'yan sanda ne da aka horar a Makarantar Horar da ’Yan sanda da ke Ikeja, Legas.

“A halin yanzu, Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin da nufin gano matakinsa na laifi da kuma yiwuwar cafke wasu da ake zargi.

“Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen kiran mutane da suka halarci harin na ranar 5 ga Afrilu da kuma fursunonin da suka tsere da su mika kansu, in ba haka ba za a sanya su fuskantar fushin doka idan aka kama su.

"Don haka, kwamishinan ya bukaci jama'a da su hada hannu da rundunar ta hanyar bayar da sahihan bayanai ga 'yan sanda, wanda hakan na iya kaiwa ga cafke masu aikata laifuka a ciki da wajen jihar."

KU KARANTA: Dawo-dawo: Matasan Najeriya Sun Kudiri Aniyar Tarawa Jonathan Kudin Takara a 2023

A wani labarin, Bayan ingantattun bayanan sirri, sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun yi ruwan bama-bamai kan tarin mayakan Boko Haram a kauyen Dawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta tattaro cewa 'yan ta’addan suna shirin kai hare-hare ne a kewayen Maiduguri lokacin da Sojojin Najeriya suka kai hari da manyan bindigogi a sansaninsu.

Wani jami’in leken asirin soja da ke cikin aikin ya fada cewa sojojin sun fara kai hare-haren ne bayan da suka samu bayanan sirri kan motsin mayakan da kuma kutse ta hanyar sadarwar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel