Najeriya na da sama da Dala Biliyan 46 a asusun kudin kasar waje - CBN

Najeriya na da sama da Dala Biliyan 46 a asusun kudin kasar waje - CBN

- Akwai sama da Dala Biliyan 46 a Baitul-Malin kasar wajen Najeriya

- Nan da ‘dan lokaci Najeriya za ta mallaki Dala Biliyan 50 a asusun ta

- Gwamnatin Shugaba Buhari ta rage shigowa da wasu kaya cikin kasar

Mun samu labari cewa kudin kasar wajen Najeriya na ta karuwa yanzu haka bayan a da abin da kasar ta mallaka yayi kasa bayan faduwar farashin man fetur a kasuwar Duniya.

Najeriya na da sama da Dala Biliyan 46 a asusun kudin kasar waje - CBN
Kudin kasar wajen Najeriya na ta karuwa a halin yanzu

Abin da Najeriya ta ke da shi yanzu a baitul-malin ta na kudin kasar waje yah aura Dala Biliyan 50 yanzu haka da mu ke magana. Daga watan Fabrairu zuwa yanzu an samu karin sama da Dala Biliyan 3 a asusun kasar na kudin waje.

KU KARANTA: Jam'iyyar adawa na cigaba da tafka rashi a Najeriya

Hakan ya yiwu ne dai bayan bankin kasar ya rage shigo da kayan da ba a a bukata da kuma samun kudin shiga ta hanyoyin kasuwancin da ba fetur din da aka saba dogara a kai ba. Haka-zalika kuma ‘Yan kasuwa sun zuba a jari a kasar.

A watan jiya dai abin da Najeriya ta ke da shi shi ne Dala Biliyan 42.8. Yanzu dai labari ya zo mana cewa CBN na shirin samun abin da ya kusa Dala Biliyan 50. Darektan bankin Isaac Okorafor yace tsarin su ya taimakawa Najeriya kwarai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng