Daki daki: Adadin kudin shiga da kowacce jahar Najeriya ta tara a shekarar 2018

Daki daki: Adadin kudin shiga da kowacce jahar Najeriya ta tara a shekarar 2018

Wani rahoto daga hukumar tattara alkalumma ta Najeriya, NBS, ta fitar ya nuna adadin kudaden shigan da jahohin Najeriya Talatin da shida da babban birnin tarayya Abuja suka tara a shekarar data gabata ta 2018.

Sai dai wani abu dake daure kai game da wannan rahoto shine yadda rahoton ya bayyana jahar Borno duk da matsalar Boko Haram da take fama dashi, amma ta shiga gaban jahohin Ekiti, Adamawa, Yobe Taraba, Kebbi da Ebonyi wajen tara kudaden shiga.

KU KARANTA: Jerin wasu ayyuka 9 daya kamata Musulmi ya ya dage da aikatawa a Ramadan

Rahoton ya bayyana cewa jahar Borno ta tara kimanin naira biliyan shida da miliyan hamsin da biyu (N6.52bn), wanda hakan ya nuna kokarin da gwamnatin jahar keyi wajen tsantsani, tare da ririta kudaden al’ummar jahar.

A jimlace, hukumar tattara alkalumma ta bayyana cewa kafatanin jahohin Najeriya sun tara naira tiriliyan daya da biliyan goma (N1.10Tr), yayin da babban birnin tarayya Abuja ta tara naira biliyan sittin da biyar da miliyan hamsin da daya (N65.51bn).

Ga dai alkalumman adadin kudin shigar da jahohin Najeriya suka tattara a 2018 kamar yadda rahoton ya nuna Lagos N382.18 biliyan, Rivers N112.78 biliyan; Kogi N11.33 biliyan; Zamfara N8.20 biliyan; Taraba N5.96 biliyan; Sokoto N18.76 biliyan; Plateau N12.72 biliyan; Oyo N24.63 biliyan; Osun N10.38 biliyan sai Ondo N24.78 biliyan.

Sauran sun hada da Ogun, N84.55 biliyan; Niger, N10.43 biliyan Nasarawa, N7.56 biliyan; Kwara, N23.04 biliyan; Kebbi, N4.88 biliyan; Kano, N44.10 biliyan; Kaduna, N29.44 biliyan; Jigawa, N9.24 biliyan; Imo, N14.88 biliyan; da Gombe, N7.34 biliyan.

Daga karshe akwai jahar Enugu, N22.14 biliyan; Ekiti, N6.46 biliyan; Edo, N28.42 biliyan; Ebonyi, N6.14 biliyan; Delta N58.43 biliyan; Cross River, N17.55 biliyan; Borno, N6.52 biliyan, Benue, N11.21 biliyan; Bayelsa, N13..63 biliyan; Bauchi, N9.69 biliyan; Anambra, N19.30 biliyan; Akwa Ibom, N24.21 biliyan; Adamawa, N6.20 biliyan; Katsina, N6.96 biliyan; da Abia, N14.83 biliyan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng