Da dumi-dumi: Buhari ya sake nada Oloyede a matsayin shugaban JAMB, ya sanar da wasu manyan nade-nade 3

Da dumi-dumi: Buhari ya sake nada Oloyede a matsayin shugaban JAMB, ya sanar da wasu manyan nade-nade 3

  • Ma’aikatar Ilimi ta sanar da manyan nade-nade guda uku da Shugaba Buhari ya amince da su
  • An sake nada Farfesa Oloyede a matsayin Shugaban hukumar JAMB yayin da aka sake nada Farfesa Rasheed a matsayin Shugaban NUC a karo na biyu
  • Buhari ya kuma amince da sake nada Isiugo-Abanihe a matsayin Shugaban NABTEB yayin da aka nada Farfesa Mebine a matsayin sabon DG na Cibiyar Lissafi ta Kasa.

FCT Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Ishaq Oloyede a matsayin Shugaban Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) a wa’adi na biyu na shekaru biyar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban kasar ya kuma amince da nadin Farfesa Abubakar Rasheed a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) da Hamid Bobboyi a a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Kasa (UBEC).

Kara karanta wannan

Siyasa a gefe: Hotunan Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari

Da dumi-dumi: Buhari ya sake nada Oloyede a matsayin shugaban JAMB, ya sanar da wasu manyan nade-nade 3
Buhari ya sake nada Oloyede a matsayin shugaban JAMB, ya sanar da wasu manyan nade-nade 3 Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Bem Goong ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta.

Shugaba Buhari ya kuma amince da sake nada Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe a matsayin shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Kasuwanci da Fasaha ta Kasa (NABTEB) na wa'adi na biyu na shekaru hudu, Aminiya ta rahoto.

Sanarwar ta ce nadin na Oloyede da Rasheed ya fara aiki ne daga ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta, nadin Bobboyi zai fara aiki daga ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.

An nada sabon DG na Cibiyar Lissafi ta Ƙasa

A halin yanzu, Shugaban kasa ya kuma yi na'am da nadin Farfesa Promise Mebine a matsayin Babban Darakta na Cibiyar Lissafi ta Kasa na tsawon shekaru biyar.

Kara karanta wannan

Abun da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano wacce ta sace zuciyar ‘da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka

Nadin Mebine ya fara aiki daga ranar Talata 17 ga watan Agusta.

Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50% a cikin shekaru 2

A wani labari, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin karin kasafin bangaren ilimi da kashi hamsin a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Shugaban kasan ya sha wannan alwashin ne a wata takarda da ya saka hannu a gagarumin taron ilimi na duniya da ya halarta a birnin London dake Ingila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel