Ana wata ga wata: Buratai ya janye manyan jami'an tsaron ofishin NSA

Ana wata ga wata: Buratai ya janye manyan jami'an tsaron ofishin NSA

Hargitsi da rashin jituwa ya fara ne tsakanin shugabannin tsaron Najeriya. Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Yusuf Buratai da mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, manjo janar Babagana Monguno ne rashin jituwar ta gibta tsakaninsu. Abun ya yi kamari a ranar Talata ne yayin da Buratai ya janye manyan hafsoshin sojan da ke karkashin ofishin Monguno ba tare da ya maye gurbinsu da wasu ba.

Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fito ya ce Monguno ne mai bashi shawara ta musamman kan tsaron kasar nan ba, ya na rike da ofishin kuma yana halartar duk tarukan tsaron da ya kamata mai ofishin na zuwa.

Binciken da jaridar Daily Nigerian tayi, ta gano cewa kwashe sojojin da aka yi daga ofishin zai zama babban kalubale ga ofishin da ke amfani da bayanan sirri wajen ba shugaban kasan bayanai a kan tsaron kasar.

Kamar yadda majiya mai karfi ta sanar, Monguno na da matsala da sauran shugabannin tsaron ba Buratai kadai ba.

A shekaru kadan baya, yanayin hakan ya faru tsakanin Monguno da Lawal Daura, tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya. Hakan kuwa yasa aka janye duk jami'an fararen kaya da ke karkashin ofishin NSA din.

Ana wata ga wata: Buratai ya janye manyan jami'an tsaron ofishin NSA
Ana wata ga wata: Buratai ya janye manyan jami'an tsaron ofishin NSA
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje, 'yan majalisa da sarakuna sun kai wa Buhari ziyara (Hotuna)

Majiya ta cikin gida ta ce, janye Jami'an ya faru ne ba da sanin NSA din ba kuma shine mafi muni a tarihi.

Majiya mai karfi ta tabbatarwa da jaridar Daily Nigerian cewa shugaban rundunar sojin Najeriya din ya dauke Manjo Janar Adeyinka Famadewa, babban jami'in NSA din. A takaice dai Famadewa ne shugaban ma'aikatan ofishin NSA din.

Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da Manjo Janar Musa Etsu-Ndagj, Birgediya Janar Jafaru Mohammed, Kanal AA Ibrahim da kuma SS Shehu.

Bayan tsananin kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta, janye manyan jami'an wannan ofishin na iya zama koma baya ga tsaron kasar nan.

Majiya daga cikin gida sun ce dama tuni shugabannin tsaron ke kallon ofishin NSA din ba a bakin komai ba saboda sun saba yin biris da ofishin koda ya kira taro.

"Wannan ne karo na farko da aka janye manyan jami'an ofishin NSA din. Wannan kuwa ya biyo bayan hargitsi da rashin jituwar da ke tsakanin Monguno ne da Buratai." Cewar majiyar.

Duk kokarin samun martani daga ofishin NSA din ya gagara.

Hakazalika mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya ki cewa komai a kan maganar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel