Gwamnati Ta Saki Sunayen Mutane 48 da Ke Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta sabunta jerin sunayen mutane da ƙungiyoyi 48 da aka ayyana a matsayin wadanda ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci
- An dauki wannan matakin ne da nufin toshe hanyoyin samun kuɗaɗe, kadarori, da duk wani tallafi da ke taimaka wa masu tada ƙayar baya
- Jerin sunayen ya haɗa da fitattun ƙungiyoyi irin su ISWAP, Ansaru, da IPOB, tare da mutane irin su Tukur Mamu, Fatima Ishaq da sauran su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabon jerin sunayen ƴan Najeriya da ƙungiyoyin da aka sanyawa takunkumi saboda zargin su da tallafa wa ayyukan ta'addanci a shekarar 2026.
Gwamnati ta dauki wannan mataki ne a ƙoƙarin da take yi na tarwatsa hanyoyin samar da kuɗaɗe ga masu tayar da ƙayar baya domin ƙarfafa tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan
Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan

Source: Twitter
Jerin mutanen da ke daukar nauyin ta'addanci
Hukumar da ke sanya takunkumi ta ƙasa (NSC), wadda ke ƙarƙashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shari'a, ita ce ta fitar da jerin sunayen a shafinta na intanet.
Ga jerin sunayen mutane da ƙungiyoyin kamar yadda hukumar NigSac ta wallafa su:
- Abdulsamat Ohida
- Mohammed Sani
- Abdurrahaman Abdurrahaman
- Fatima Ishaq
- Tukur Mamu
- Yusuf Ghazali
- Muhammad Sani
- Abubakar Muhammad
- Sallamudeen Hassan
- Adamu Ishak
- Hassana Isah
- Abdulkareem Musa
- Umar Abdullahi
- Abdurrahaman Ado
- Bashir Yusuf
- Ibrahim Alhassan
- Muhammad Isah
- Salihu Adamu
- Surajo Mohammad
- Fannami Bukar
- Muhammed Musa
- Sahabi Ismail
- Mohammed Buba
- Adamu Hassan
- Hassan Mohammed
- Usman Abubakar
- Kubara Salawu
- Rabiu Suleiman
- Simon Njoku
- Godstime Iyare
- Francis Mmaduabuchi
- John Onwumere
- Chikwuka Eze
- Edwin Chukwuedo
- Chiwendu Owoh
- Ginika Orji
- Awo Uchechukwu
- Mercy Ali
- Ohagwu Juliana
- Eze Okpoto
- Nwaobi Chimezie
- Ogumu Kewe
- Jama'atu Wal-Jihad
- Ansarul Sudan (Ansaru)
- Islamic Province (Iswap)
- Indigenous Biafra (Ipob)
- Yan Group
- Yan Group Nlbdg

Source: Twitter
Muhimmancin wannan mataki ga tsaron kasa
Wannan mataki ya yi daidai da dokar hana ta'addanci ta shekarar 2022. Babban burin gwamnati shi ne tabbatar da cewa ba a bar masu tallafa wa ta'addanci su yi amfani da tsarin hada-hadar kuɗi na duniya wajen janyo rashin zaman lafiya a ƙasar ba, cewar rahoton da aka wallafa a shafin cibiyar PLAC.
Gwamnatin Najeriya, a matsayinta na mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya, ta jaddada aniyarta na bin dukkan matakan diflomasiyya da na shari'a domin toshe hanyoyin da ƴan ta'adda ke bi wajen siyan makamai da gudanar da ayyukan da ke barazana ga rayukan ƴan ƙasa.
Wannan bincike zai shafi dukkan mutane da ƙungiyoyin da aka tabbatar suna da hannu a ayyukan ta'addanci ba tare da nuna bambanci ba.
Mutane 16 masu tallafawa 'yan ta'adda
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta ayyana Simon Ekpa, kungiyar Lakurawa da wasu mutum 14 a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci.

Kara karanta wannan
Wahalar da na sha a APC ko shugaban jam'iyya bai sha ba in ji Diyar Buba Galadima
An bukaci bankuna da cibiyoyin kasuwanci su toshe duk wasu kudi ko kadarori da ke da alaka da mutanen da aka bayyana a jerin.
Sunayen da aka fitar sun hada da Ekpa, Godstime Promise Iyare, da wasu kamfanoni kamar Igwe Ka Ala Enterprises da Seficuvi Global.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
