Dalla Dalla: Hanyoyin da Dalibai Za Su Bi domin Yin Rajistar Jarabawar UTME 2026
Abuja - Hukumar da ke kula da jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta saki bayanai da hanyoyin da dalibai za su bi domin yin rajistar jarabawar UTME ta shekarar 2026.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan ya kunshi matakan da za a bi, kura-kuran da za a kiyaye da kuma kalubalen da dalibi zai iya fuskanta yayin rajistar jarabawar UTME.

Source: Facebook
Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar JAMB ta wallafa wadannan bayanai ne a shafinta na X a ranar Lahadi, 7 ga watan Disamba, 2025.
A cikin sanarwar, JAMB ta jaddada cewa dole ne dalibai sun tabbatar da cewa dukkanin bayanansu, musamman da suke da alaka da lambar NIN dinsu, sun zamo iri daya, kafin fara rajistar UTME 2026.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda dalibai za su hada bayansu da UTME
Abu na farko da ake so dalibi ya yi shi ne ya tabbatar da cewa bayansa da ke a hukumar NIMC da sauran hanyoyin tantance shi, misali, shaidar kammala karatun firamare, sakandare, duka sun zama iri daya.
Idan ya tabbatar da hakan, to sai ya fara aika wannan sako: NIN (a bar tazara) sannan a rubuta lambar NIN guda 11. A aika sakon ga 55019 ko 66019. Misali, NIN 00000011111 zuwa ga 55019 ko 66019.
JAMB ta yi gargadi cewa daga lokacin da aka aika wannan sako, to an bude wa dalibi bayansa a UTME, kuma ba zai iya canja komai ba, domin hukumar za ta dauko bayansa kai tsaye daga shafin NIMC.
Ga hanyoyin yin rajistar UTME 2026
Hukumar JAMB ta fitar da matakan da za a yi rajistar UTME 2026 kamar haka:
1. A ziyarci cibiyar JAMB/CBT mafi kusa
An bukaci dalibai su ziyarci ofishin hukumar JAMB ko kuma wata cibiyar CBT mafi kusa domin fara rajistar UTME 2026.
2. Sayen kati/lambar E-PIN
An bukaci dalibai su sayi lamba ko kuma katin e-Pin daga wuraren da aka sahale masu kamar bakuna, dillalai da shafukan intanet da aka amince da su.
3. Yi rajista a fom din da ya dace
JAMB ta jaddada bukatar dalibai su cike bayansu yayin rajista a fom din da ya dace, ba wai na buga-buga ba.
4. Tura bayanai
Bayan dalibai sun kammala cike dukkan bayanansu, an bukace su su tabbatar komai nasu ya yi daidai kafin su tura amincewar rajistarsu a cibiyar da suke yin rajistar.
Wasu muhimman bayanai ga dalibai
JAMB ta kuma fitar da wasu muhimman bayanai, da suke kama da gargadi ga dalibai:
1. Dole dalibai su yi duk wasu gyare-gyaren bayanansu a shafin NIMC da wuri, misalin gyaran suna, ranar haihuwa, jinsi, jihar haihuwa, kuma a tabbatar an sabunta gyaran a shafin NIMC.
2. Ya zama dole a yi amfani da lambar waya da imel da ke aiki, domin su ne ginshikin wannan rajistar.
3. Daliban da suke fuskantar matsaloli na bayanan yatsunsu, su ziyarci ofishin JAMB mafi kusa.
4. A yi amfani da komfuta mai fuska biyu yayin rajista ta yadda dalibi zai rika kallon bayanan da ake cike masa, da kuma hotonsa da aka dauka.
UTME: Matsalolin da aka fi fuskanta

Source: Facebook
JAMB ta kuma yi bayani game da wasu matsaloli da dalibai kan fuskanta yayin rajistar wannan jarabawa:
1. “Record Not Found”
Hanyar gyara wannan matsala: Dalibi ya ziyarci hukumar NIMC mafi kusa domin gyara bayanansa da tabbatar da cewa sun hau.
2. “Wrong Parameter”
Wannan dai na nufin cewa bayanan da aka shigar a lokacin tura sako ga 55019 ko 66019 ba daidai ba ne.
Hanyar gyara wannan matsala: A sake aika sako a tsarin da yake dai dai, misali: NIN 00000011111.
3. “Your NIN has already been registered with GSM number…”
Wannan na nufin cewa, an riga da an yi amfani da NIN dinka a wata lambar wayar, kuma har an shigar da bayanan.
Hanyar gyara wannan matsala: Ka nemo asalin layin wayar da aka tura NIN din, domin sake tura wannan sako.
4. “Unable to verify your NIN at the moment [NIMC: UNKNOWN]”

Kara karanta wannan
CBN ya kawo sabuwar doka kan ajiya da cire kudi a Najeriya, za ta fara aiki a 2026
Wannan na nufin, shafin NIN ba zai iya shigar da bukatarka ta karbar NIN a lokacin ba.
Hanyar gyara wannan matsala: A dan jira, sannan a sake jarabawa bayan wani dan lokaci.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa daga Janairun 2026 ne JAMB za ta fara sayar da fom din zana jarabawar UTME 2026 har zuwa Maris din shekarar.
An fitar da sakamakon UTME 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, JAMB ta fitar da sakamakon UTME na 2025, amma ta riƙe sakamakon dalibai 39,834 saboda matsalolin da suka shafi kura-kuran jarrabawa.
Hukumar JAMB ta ce tana binciken mutane 80 da ake zargi da maguɗin jarrabawa, inda jihar Anambra ke da mafi yawan waɗanda ake zargi da aikata wannan laifi.
Shugaban JAMB, Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa dalibai 467 da ba su kai shekaru 18 ba sun samu maki kadan, amma 50 sun aikata ba daidai ba yayin zana jarabawar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


