Yadda ake amfani da manhajar katin dan kasa (NIMC)

Yadda ake amfani da manhajar katin dan kasa (NIMC)

- NIMC ta bayyana ta samar da hanya mafi sauki wajen amfani da katin dan kasa

- NIMC din sun sake sabuwar manhaja don ganin bayanai na jikin katin dan kasar

- Hukumar ta bayyana hakan a matsayin ci gaba ta fuskar fasahar zamani

Mataimakin mai kula da harkokin fasaha, na fasahar sadarwa a Ma’aikatar Sadarwa, Femi Adeluyi, ya yi bayani a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Alhamis, 31 ga Disamba, 2020, a Abuja.

Hukumar NIMC ta kirkiri wata manhajar wayar hannu da za a iya ganin bayanan katin dan kasa.

Ya ce ci gaban na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na inganta tsarin samun NIN da kuma danganta shi da layukan waya, da kuma daidaito da tsarin tattalin arzikin kasa na zamani na Najeriya, kamar yadda wakilin Legit ya ruwaito.

KU KARANTA: Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa

Yadda ake amfani da manhajar katin dan kasa (NIMC)
Yadda ake amfani da manhajar katin dan kasa (NIMC) Credit: Android Play Store
Source: UGC

Game da manhajar

NIMC ta ce manhajar na da sauƙin sarrafawa da kyan gani.

A bisa wani sharadi, dole ne mutumin da yake son amfani da shi ya samu NIN dinsa domin samun damar amfani da shi a wayar hannu.

Yadda za a sauke manhajar

Masu amfani da wayar Android da masu amfani da wayar iPhone zasu iya sauke manhajar wayar hannun akan Google Play Store da Apple App Store. Sa'an nan su bi wadannan matakan:

1. Bayan saukewa da daura manhar a waya, a yi duba zuwa hagu a danna Skip da Begin

2. A sanya lambobi 11 na NIN a latsa Next, sannan daga nan a latsa I Agree

3. Bayan mataki na biyu, lambar wayar da ayi amfani da ita wajen yin rijistar NIN zata fito tare da tambayoyi biyu;

a. Har yanzu ina amfani da wannan Lambar Wayar

b. Bana amfani da wannan lambar

4. Danna maɓallin da yake daidai daga tambayoyin biyu sannan a latsa Next

5. Idan lamba daya ake amfani da ita, a shigar da user ID da OTP din da aka aiko zuwa wayar ta hanyar SMS. Sannan danna Proceed

6. Idan ba a amfani da lambar yanzu, a ziyarci kowane ofishin NIMC don sabunta lambar wayar

KU KARANTA: Haɗari ne gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta

A wani labarin, NIMC, hukumar da gwamnatin tarayya ta dorawa alhakin bayar da katin dan kasa, ta kirkiri sabuwar manhajar wayar hannu domin amfanin 'yan kasa, kamar yadda BBC ta rawaito.

Hukumar ta bukaci 'yan Nigeria su sauke manhajar a wayoyinsu na hannu domin samun saukin tafiya da shaidarsu ta zama 'yan kasa a cikin wayar salula koda yaushe, Kuma a duk inda suke.

A cikin watan Disambar na shekarar 2020 ne hukumar NCC ta bukaci kamfanonin sadarwa su hada lambobin wayar 'yan kasa da lambar tantancewa da NIMC ta bayar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel