Wasu Fusatattun Ɗalibai Sun Yi Fata-Fata da Cibiyar Zana Jarabawar JAMB CBT

Wasu Fusatattun Ɗalibai Sun Yi Fata-Fata da Cibiyar Zana Jarabawar JAMB CBT

  • Hukumar tsaro ta NSCDC ta samu nasarar damƙe wasu ɗalibai huɗu da take zargin sun lalata cibiyar rubuta jarabawa CBT a Otuoke
  • Kwamandan jami'an NSCDC ta jihar Bayelsa, Mrs Christiana, ita ce ta bayyana haka ga manema labari
  • Hukumar JAMB ta saki sakamakon jarabawar bana UTME 2021, tace babu dalilin da zai sa ta rike sakamakon

Hukumar tsaro ta NSCDC da cafke wasu ɗalibai dake zana jarabawar JAMB da zargin lalata wata cibiyar jarabawar na'ura mai ƙwaƙwalwa (CBT) a Otuoke, jihar Bayelsa, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB Ta Fara Sakin Sakamakon Jarabawar UTME 2021

Da take jawabi ga manema labarai a Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa, kwamandan jami'an NSCDC, Mrs Christiana Abiakam-Omanu, tace an kama waɗanda ake zargin ne a cibiyar CBT dake jami'ar tarayya dake Otuoke.

Kwamandan ta ƙara da cewa hukumar NSCDC ba zata lamurci lalata kayayyakin da suke mallakin gwamnati ba.

Hukumar NSCDC ta cafke wasu ɗalibai 4
Wasu Fusatattun Ɗalibai Sun Yi Fata-Fata da Cibiyar Zana Jarabawar JAMB CBT Hoto: Jamb.gov.ng
Asali: UGC

Ta bayyana cewa waɗanda ake zargin sun kawo cikas a jarabawar dake gudana a cibiyar, sannan kuma sun lalata wasu daga cikin kayan aiki a wurin ranar Talata.

Mrs Christiana tace an bar daliban sun gama rubuta jarabawarsu kafin daga bisa aka tasa keyar su.

Tace: "A halin yanzun muna cigaba da bincike domin zaƙulo sauran waɗanda suke da hannu a lamarin."

"Ɗalibai huɗu muka kama, kuma duka sun amsa laifin da ake zarginsu, sun roƙi gwamnati ta yi musu afuwa."

KARANTA ANAN: Mun Gano Wani Mummunan Shiri da Aka Shirya Mana Kan Jarabawar Bana 2021, Shugaban JAMB

JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME 2021

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB, tace zata fara sakin sakamakon jarabawar UTME 2021 daga ranar Laraba 23 ga watan Yuni.

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyade, shine ya bayyana a wurin taron manema labarai a jihar Enugu.

A wani labarin kuma Sanatoci Zasu Fallasa Sunayen MDAs da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

Sanatoci zasu fara bayyana duk wata hukuma ko ma'aikatar gwamnati da ta gaza kare zargin da ake mata, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban Sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, shine ya bayyana haka bayan gabatar da rahoton kwamiti.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel