Tashin Hankali: Saurayi Ya Cinna wa Tsohuwar Budurwarsa Wuta a Barikin Sojoji
- Jami'an tsaro sun kama Lawal Faruq, saurayin da ake zargin ya babbake tsohuwar budurwarsa, Omolola Hassan, a Ibadan
- Shaidu sun ce sojoji ne suka ceci wadda abin ya shafa sannan suka garzaya da ita asibitin, sannan aka kama wanda ake zargi
- Lawal Faruq dai ya fito ya bayyana dalilin da ya sa ya bulbulawa tsohuwar budurwarsa fetur, ya cinna mata wuta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Rahotanni daga jihar Oyo na nuni da cewa rundunar 'yan sanda ta cafke wani mutumi, Lawal Faruq, bisa zargin kone tsohuwar budurwarsa.
An rahoto cewa Lawal Faruq ya dauki doka a hannunsa bayan da budurwar tasa ta yanke alakar soyayyar da ke tsakaninsu, inda ya cinna mata wuta.

Source: Getty Images
Saurayi ya kona tsohuwar budurwarsa
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a cikin rahoton da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, ya nuna cewa Lawal ya cinnawa tsohuwar budurwarsa wuta a barikin sojoji na Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Lawal Faruq dai ya hau dokin zuciya ne bayan soyayya ta zo karshe tsakaninsa da budurwar, alhalin a cewarsa, sun yi alkawarin kasancewa da juna har abada.
A cewar Lawal, bakin cikin rabuwa da ita, da kuma tuna alkawarin da suka yi ne ya sanya shi bulbula mata fetur, ya kyasta mata ashana ta kama da wuta.
Sojoji sun cafke saurayin Omolola
A lokacin da budurwar ta fara ci da wuta, an ce wasu jami'an sojoji da ke a barikin ne suka kai mata dauki, suka garzaya da ita asibiti, tare da cafke Lawal.
Jaridar ta rahoto cewa:
"Majiya ta ce wanda ake zargi ya bulbulawa Omolola Hassan fetur tare da cinna mata wuta, saboda takaicin ta daina soyayya da shi.
"A cewar wadanda abin ya faru a kan idonsu, sojojin da ke a barikin ne suka hanzarta kai dauki tare da kashe wutar, kafin su garzaya da ita asibitin Yawiri da ke Akobo.
"Yanzu haka, wanda ake zargin, da ya yi ikirarin cewa sun yi alkawari da juna cewa mutuwa ce za ta raba su, yana hannun jami'an tsaro."
'Yan sandan Oyo sun yi martani
Da yake martani bayan jaridar Punch ta tuntube shi kan lamarin, kakakin 'yan sandan Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Osifeso ya yi nuni da cewa yanzu haka ana gudanar da bincike kan labarin, kuma za a fitar da rahoto da zarar an samu karin bayanai.
"Yanzu haka muna kan gudanar da bincike,' Osifeso ya ba da amsar wani sako da aka aika masa kan lamarin.
Ana ci gaba da samun ire-iren wadannan ta'addancin, idan masoya kan illata ko hallaka masoyansu idan soyayyar ta kare.

Source: Original
Yadda ake samun rikicin masoya a Najeriya
Ko a watan Yulin 2025, an rahoto cewa wata dalibar jami'ar Fatakwal, Cynthia Chukwundah, ta cinnawa masoyinta wuta yayin da suke cacar baki game da cikin da ta yi. An ce saurayin ya mutu daga kunar wutar.
A watan Janairun 2023, an rahoto cewa wani mutumi ya makure wuyar budurwarsa, sannan daga bisani ya cinna mata wuta saboda zargin ita juya ce a jihar Rivers.
Hakazalika, a Afrilun shekarar, wani dan shekara 42 ya shiga hannun hukuma a Ogun bisa laifin cinnawa gidan tsohuwar budurwarsa wuta saboda taki yarda su daidaita kansu.
Saurayi ya kashe budurwarsa kan jima'i
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani dan shekara 19, Muhammad Ibrahim ya kashe budurwarsa saboda ta nemi ya biya ta kudin gamsar da shi.
Hatsaniya kan biyan kudin ta kaure tsakanin masoyan har ta kai ga doki-in-doke ka, abin ya zo da karar kwana Ibrahim ya daba wa budurwar wuka.
Duk da kokarin jama'a na ceton budurwar, rai ya yi halinsa, inda shi ma Ibrahim ya gamu da fushin mutane, amma 'yan sanda suka cece shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

