Budurwa ta banka wa saurayinta wuta saboda ya ki aurenta (Hotuna)
- Bai wuce makonni 2 da labarin wata budurwa wacce ta bankawa gidan saurayinta wuta a Legas ya karade duniya ba
- Sai ga wata budurwar 'yar jihar Benue ta bankawa gidan iyayen saurayinta wuta saboda ya fasa aurenta
- Cikin gidan akwai mahaifiyar saurayin, saurayin da kuma wani karamin yaro, sai dai duk sun ji rauni amma babu wanda ya mutu
Bai wuce makonni 2 kenan da wata budurwa ta banka wa saurayinta wuta a Festac, jihar Legas ba. Wata budurwa ta kona nata saurayin a gidansa da ke layin Shaahu da ke karamar hukumar Gboko, a jihar Benue a kan kin aurenta da yayi.
Ganau sun tabbatar da yadda budurwar ta banka wa gidan wuta da misalin 1:30am a ranar Litinin, bayan saurayin mai suna Jude, mahaifiyarsa da wani karamin yaro sun kwanta barci, Vanguard ta ruwaito.
Kamar yadda ganau suka shaida, an ci babbar sa'a tunda babu wanda ya mutu cikinsu, amma saurayin ya kone sosai. Mahaifiyarsa da yaron kuwa tasu kunar bata da yawa, amma duk suna asibitin Gboko ana kulawa da lafiyarsu.
"Mun gano cewa Jude ya fasa auren budurwar sakamakon wata hayaniya da ta hadata da mahaifiyarsa, sai ya koreta daga gidan.
"Da safiyar Litinin, budurwar ta kwaso wasu mutane, inda suka watsa wa gidan fetur, suka banka wuta. Sai dai makwabtansu suka yi gaggawar kai musu dauki," yace.
Bayan tattaunawa da jami'in hulda da jama'an hukumar 'yan sandan, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Anene ta ce sun samu labarin faruwar lamarin, amma har yanzu ba a ga yarinyar da tayi aika-aikar ba.
KU KARANTA: Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa
KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)
A wani labari na daban, wata mata ta maka saurayinta a kotu sakamakon bata mata lokaci duk da shekarunsu 8 tare amma ya gaza aurenta.
Ngoma ta sanar da wata kotu a Zambia cewa ta gaji da jiran Herbert Salaliki mai shekaru 28, wanda yayi mata alkawarin aure.
A cewar Mwebantu, har yanzu Ngoma tana zaune da iyayenta duk da ta haifa wa Herbert da guda daya, shi kuma yana zaman kansa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng