Majalisa Ta Yarda Tinubu Ya Kashe N140bn, za a Yi Aiki a Abuja da Jihohin Arewa 6
- Majalisar dattawa ta amince gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kashe Naira biliyan 140 matsayin kasafin hukumar NCDC
- NCDC ce ke kula da raya shiyyar Arewa ta Tsakiya, wacce ta kunshi Abuja da jihohin Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateau
- Shugaba Bola Tinubu ya warewa NCDC kasafin Naira biliyan 140 a 2025 don gudanar da manyan ayyuka da na yau da kullum
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya za ta kashe Naira biliyan 140 na kasafin kudin hukumar raya shiyyar Arewa ta Tsakiya (NCDC) na 2025.
Kwamitin majalisar dattawa da ke kula da hukumar NCDC ne ya amince da kasafin kudin hukumar na 2025 da ya kai Naira biliyan 140.

Source: Twitter
Majalisa ta amincewa NCDC kasafin N140bn
Amincewa da kasafin kudin ya biyo bayan zama da Tsenyil Yiltsen, shugaban NCDC, inda ya kare kasafin a gaban kwamitin a ranar Talata, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Titus Zam, shugaban kwamitin ya ce majalisar dattawa ta amince da kasafin ne bayan kyayyawan nazari da kuma bayanan da shugaban NCDC ya yi.
"Bayan nazari mai kyau kan abubuwan da ke kunshe a kasafin da kuma yadda shugaban hukumar da tawagarsa suka gabatar da jawabai, kwamitin ya amince da kasafin Naira biliyan 140 ga hukumar."
- Sanata Titus Zam.
A yayin gabatar da jawabi, Tsenyil Yiltsen ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ce ta ware Naira biliyan 140 matsayin kasafin NCDC na shekarar 2025.
Ayyukan da NCDC za ta yi da N140bn
Ya ce za a yi amfani da Naira biliyan 100 wajen gudanar da manyan ayyuka a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihohi shida na Arewa ta Tsakiya.
Hazalika, za a yi amfani da Naira biliyan 40 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum, da suka hada da kudin gudanar da ayyuka da kula da ma'aikata.

Kara karanta wannan
Rubutu kan Tinubu ya jawo an maka tsohon 'dan takarar shugaban kasa a kotun Abuja
This Day ta rahoto Tsenyil Yiltsen ya bayyana cewa ba wai za a kashe wadannan biliyoyin kudin ga aiki guda daya kawai ba, illa dai za a yi ayyuka masu yawa a shiyyar.
"Muna da bangarori takwas a bangaren ci gaban Arewa ta Tsakiya da suka hada da tsaro, noma, hakar ma'adanai, ci gaban yanki, ilimi, kiwon lafiya da tituna."
- Tsenyil Yiltsen.

Source: Facebook
Za a dauki sababbin ma'aikata a NCDC
Shugaban NCDC ya tabbatarwa kwamitin majalisar cewa za a gudanar da wadannan ayyuka ne dai dai wadaida tsakanin jihohi shida da Abuja.
"Za mu fita mu yi binciken ayyukan da kowace jiha take bukata, kuma za mu raba ayyukan ne bisa adalci tsakanin Abuja da jihohin shiyyar shida," inji Tsenyil Yiltsen.
Shugaban NCDC ya kuma yi nuni da cewa za a yi amfani da wani bangare na Naira biliyan 40 don ayyukan yau da kullum kamar biyan albashin akalla ma'aikata 200 da kuma daukar sababbin ma'aikata.
Tinubu ya sanya hannu kan dokar NCDC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar kafa hukumar raya shiyyar Arewa ta Tsakiya (NCDC.

Kara karanta wannan
"A tsage biri har wutsiya": Lauya ya nemi bayani a kan kudin da Remi Tinubu ta tara
Ana sa ran dokar kafa NCDC za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan ci gaba a Abuja da jihohi shida na Arewa ta Tsakiya.
Baya ga dokar kafa NCDC, Tinubu ya kuma amince da kafa kwalejin kimiyya a Rano (jihar Kano), da jami’ar lafiya a Tsafe (jihar Zamfara).
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
