Da Gaske ne, Gwamna Ya Haramta Wa'azi da Hudubar Juma'a sai da Izini a Jihar Neja

Da Gaske ne, Gwamna Ya Haramta Wa'azi da Hudubar Juma'a sai da Izini a Jihar Neja

  • Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya bayyana cewa wajibi ne malamai su gabatar da hudubarsu kafin a ba su izinin su yi
  • Gwamna ya ce wannan ba bakon abu ba ne, domin ko a Saudiyya ana amfani da wannan tsari don dakile hudubobi masu ta da rikici
  • Yayin da gwamnan ya kare matakin da ya dauka, wasu malaman Musulunci suna ganin hakan ya tauye ‘yancin addini da yada shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Gwamna Umaru Bago ya fayyace dokar da gwamnati ta bullo da ita domin daidaita harkokin wa’azi a jihar Neja.

Ya ce gwamnati ba ta haramta wa’azi gaba ɗaya ba, sai dai ta yi doka cewa malaman addini su gabatar da hudubarsu kafin su yi amfani da ita a masallatai ko coci.

Kara karanta wannan

Jarumin Kannywood ya fadi halin jinya da yake ciki, ya yaba gudunmawar Ali Nuhu

Gwamna Umar Bago ya ce dole limami su fara gabatar da hudubobinsu a tantance kafin su yi a jihar Neja
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago yana jawabi a wata cocin Living Faith da ke Minna. Hoto: @GovNigerNG
Source: Twitter

'Sai mun tantance za a yi huduba' - Gwamna Bago

Gwamna Umar Bago ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a shirin 'Siyasa a ranar Lahadi,' na gidan talabijin TVC a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna jihar na Neja ya ce:

“Ba mu hana wa’azi gaba ɗaya ba. Amma duk wanda zai yi huduba ranar Juma’a ko Lahadi ya kawo mana mu duba, mu tantance.
"Wannan abu ne na yau da kullum. Ko a Saudiya haka ake yi. Ba za mu bar wani ya yi wa’azi da zai yi adawa da jama’a ko gwamnati ba."

Gwamnan ya bayyana cewa wannan tsari yana da nasaba da tsaro da kare jama’a daga kalaman da ka iya tada fitina, tare da haɗin gwiwar DSS, ƴan sanda, NSCDC da sojoji.

Neja: Malamai za su nemi lasisin wa'azi

Daraktan kula da harkokin addini na jihar Neja, Umar Farooq, ya ce dole ne duk wani malami da ke son yin wa'azi ya samu lasisi a cikin watanni biyu.

Kara karanta wannan

Za ayi nasara, Gwamna Dikko Radda ya fadi babbar hanyar kawo karshen ta'addanci

Umar Farooq ya ce malamai za su cike fom sannan kwamiti na musamman da aka kafa zai tantance su kafin a basu lasisin yin wa'azi.

"Eh da gaske ne, gwamnatin jihar ta haramta yin wa'azi. Duk malamin da ke son ya yi wa'azi zai nemi lasisi daga nan zuwa watanni biyu masu zuwa.
"Abin da kawai suke bukata shi ne, su zo ofishinmu, su cike fom. Bayan nan, za su bayyana gaban kwamitin da zai tantance su, kafin su fara wa'azi."

- Umar Farooq.

Gwamna Umaru Gabo ya ce dokar ba da lasisin wa'azi a Neja zai dakile wa'azin da zai haifar da tashin hankali a jihar.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago yana jawabi a ziyarar da ya kai cocin RCCG da ke Minna. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Martanin Malamai da kungiyoyin addini

Babban limamin Jami’a na jami'ar FUT da ke Minna, Bashir Yankuzo, ya ce wa’azi ibada ce kuma gwamnati ba ta da hurumin hana wa’azi.

Sai dai ya amince cewa gwamnati na iya sa baki idan aka yi amfani da wa’azi wajen tayar da hankalin jama’a, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sakataren CAN reshen Neja, Raphael Opawoye, ya ce ba a sanar da su hukuncin gwamnatin ba tukuna, amma za su fito da matsayinsu idan aka yi hakan.

Sai dai wani malamin addini, Uthman Siraja, ya ce wannan mataki kutse ne ga ‘yancin addini, inda ya ba da shawarar a hukunta malamai da suka saba ka'idojin wa'azi maimakon hana wa’azi gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Shirin da Gwamna Abba Kabir ya yi kan auren jinsi a Kano

Gwamna ya hana wa'azi a bainar jama'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya hana wa’azi da lasifika a kasuwanni, abin da ya kira da 'haniya'.

A wani bidiyo da ya yadu, an ga Soludo yana dakatar da wani mai wa’azi a kasuwa, yana umurtarsa da ya guji tayar da hayaniya a wajen.

Tsohon gwamnan CBN ya bayyana cewa duk wanda ya karya dokar zai biya tarar N500,000, ya ba da shawara a yi wa’azi a coci ko wasu wurare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com