An Yi Babban Rashi a Katsina, Diyar Mai Martaba Sarki Ta Rigamu Gidan Gaskiya

An Yi Babban Rashi a Katsina, Diyar Mai Martaba Sarki Ta Rigamu Gidan Gaskiya

  • Gwamna Dikko Radda, shugaban 'yan sanda, daraktan DSS, Dahiru Mangal da wasu kusoshi sun cika fadar Sarkin Katsina
  • An rahoto cewa, dubunnan mutane ne suka yi dafifi a fadar, domin halartar jana'izar diyar Sarkin Katsina, Khadija Abdulmumini
  • Khadija, wacce aka fi sani da Andijo, mai shekaru 35 ta rasu ne a Abuja, kuma mutuwarta ta jefa masarautar Katsina cikin jimami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya yi rashin ’yarsa, Khadijah Abdulmumin Kabir Usman, wacce ta rasu a Abuja tana da shekara 35.

Marigayiya Khadijah, wacce ake kira Andijo, ta kasance abar kauna ga kowa a gidan sarautar, kuma ta rasu ta bar yara uku.

Diyar sarkin Katsina, Khadijah Abdulmumin Kabir Usman ta rasu, Dikko Radda ya halarci jana'iza
Diyar Sarkin Katsina, Khadija da ta rasu da manyan Katsina a wajen jana'izar 'yar sarkin. Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

An yi jana'izar diyar Sarkin Katsina

Wannan mutuwa ta jefa masarautar Katsina cikin jimami, inda daruruwan jama’a suka garzaya fadar sarki don yin ta’aziyya, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Sanata ya maka gwamnan Kaduna a kotun duniya, yana so a cafke Uba Sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da sallar jana’izar Khadija a fadar sarkin Katsina, karkashin jagorancin Liman Mustapha Gambo.

An rahoto cewa Gwamna Dikko Umaru Radda, manyan sarakuna, jami’an gwamnati, da attajirai sun halarci wannan sallar jana'aiza.

Bayan kammala sallar ne aka wuce da gawar zuwa makabartar Dan Takum, inda aka binne, tare da daukar lokaci ana yi mata addu'a ta samun rahamar Allah.

Mai magana da yawun gwamna, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, Radda ya halarci jana’iza da zaman gaisuwa don ya karfafi Mai martaba sarki.

Gwamna ya yi ta'aziyyar diyar Sarkin Katsina

Sanarwar ta ce Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin mutumiyar kirki kuma uwa ta gari ga 'ya'yanta, wadda ta taimaki mutane da dama a lokacin da take raye.

A cewar gwamnan, mutuwar Khadijah babban rashi ne ga iyalinta da kuma masarautar Katsina baki ɗaya.

Gwamnan ya roƙi Allah ya gafarta mata laifuffukanta, ya karɓi ayyukan alherinta, ya kuma sanya ta a cikin Aljannatul Firdausi.

Kara karanta wannan

Harin masallaci: Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau, ya dauki alkawura

Haka kuma ya yi addu’a ga yaran da ta bari, yana neman Allah ya yi musu jagora da kariya cikin rayuwarsu.

Ya shawarci iyalan Mai martaba sarkin da su rungumi kaddara, yana mai tunatar da su cewa rai da mutuwa dukkansu suna a hannun Allah ne.

Gwamna Dikko Radda ya karfafi sarkin Katsina a yayin da diyarsa Khadija ta rasu
Gwamnan Dikko Radda, mataimakin gwamna, Faruk Jobe, suna ta'aziyyar diyar Sarkin Katsina. Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Kusoshi sun halarci jana'izar diyar sarki

Sanarwar ta ce:

"Zuwan Gwamna Radda wajen jana'izar ya sake nuna irin kusancinsa da masarautar Katsina da kuma girmamawar da yake yi wa masarautun gargajiya.
"Sakon ta'aziyyarsa da addu'o'in da ya yi, ya samar da wani sassauci ga iyalan mai martaba sarkin yayin da suke cikin jimami na wannan babban rashi."

Taron jana’izar ya samu halartar mataimakin gwamna Faruk Jobe, attajirin dan kasuwa, Dahiru Mangal, da kwamishinan ’yan sanda Bello Shehu.

Haka kuma daraktan DSS, Jabiru Tsauri, Lamidon Katsina, Abba Jaye, Dan Malikin Katsina, da Wazirin Katsina, Alhaji Ida, duk sun halarta.

Sarkin Katsina ya ba dan gwamna sarauta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman ya sanar da naɗin sababbin hakimai shida a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Katsina na gunaguni, Gwamna Radda ya dawo Najeriya amma ya tsaya a makwabta

Sakataren masarautar Katsina, Alhaji Bello Ifo ya sanar da cewa ɗan Gwamna Diko Raɗɗa na cikin waɗanda aka naɗa a matsayin hakimai.

Haka zalika, tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya zama sabon Marusan Katsina, hakimin Shargalle a ƙaramar hukumar Dutsi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com