'Matsalolin' Najeriya Na Hana Ni Barci, Har Na Kamu Da Rashin Lafiya, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman

'Matsalolin' Najeriya Na Hana Ni Barci, Har Na Kamu Da Rashin Lafiya, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman

  • Masauratar Katsina ta kaddamar da gidauniya don taimakawa gwamnati wajen rage mata nauyi sakamakon ta'addanci da ya taba sassan jihar
  • A wajen kaddamar da gidauniyar, sarkin Katsina ya ce matsalolin kasar nan suna damunsa har ta kai baya iya bacci saboda matsalar kasar
  • Kwamitin ya raba kayan tallafi ga yan gudun Hijira da marayu da mata marasa lafiya da sauran mabakata marasa karfi

Jihar Katsina - Mai martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman, ya koka kan yawan kallubalen da Najeriya ke fama da su, yana mai cewa lamarin abin damuwa ne, The Channels ta rahoto.

Sarkin Katsina
Sarkin Katsina ya kaddamar da gidauniyar zaman lafiya, ya yi rabon kayan tallafi. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

A wurin kaddamar da gidauniyar zaman lafiya da ya kafa 'Katsina Peace Foundation' a ranar Alhamis, Sarkin ya ce:

"Matsalolin Najeriya na cikin abubuwan da ke damu na har ta kai bana iya bacci tsawon kwanaki uku zuwa bakwai.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa Sun Fusata, Sun Aike da Muhimmin Sako Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A takaice, ban yi kuskure ba idan na ce sune suka janyo min jinyar da na ke fama da ita a halin yanzu."

Mutane 17000 sun amfana da tallafi daga gidauniyar zaman lafiya ta Katsina

A wajen bikin, akalla mutum 17,000 ne a fadin jihar suka amfana da rabon kayan tallafi.

Wanda suka amfana, mafi yawanci wanda wanda tashin hankali ya raba da muhallansu, marayu, mata da ke fama da cutukan yoyon fitsari na mata daga cikin sauran marasa galihu, sun amfana da buhunan masara, gero, shinkafa, sukari, atamfa, da sauran kayan da ba na abinci ba.

Sarkin, lokacin da ya ke rabon kayan ta hannun wakilan wanda suka amfana, ya ce rabon ya zama dole saboda Annabi Muhammad (SAW) ya umarci musulmi su taimaki yan uwansu musulmai, da magwabta na kusa da na nesa wanda ke da bukatu ba tare da duba bambanci ba.

Kara karanta wannan

Ramadana: Hisbah ta fasa kwalaben barasa na N500 a jihar Kano, ta yi wani bayani

Buhun shinkafa
Buhunan shinkafa da sarkin Katsina ya raba wa al'umma yayin kaddamar da gidauniyarsa. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Burin Kafa Gidauniyar Zaman Lafiya ta Katsina - Sanata Ibrahim Ida

Babban burin gidauniyar, a cewar shugaban kwamitin amintattu, kuma wazirin Katsina na shida, Sanata Ibrahim Ida, shi ne a taimakawa gwamnati don taimaka mata wajen kawo karshen ta'addanci a jihar, masarautar, da kasar gaba daya.

Sauran kudirin ya hada da taimakon wanda ta'addanci ya tagayyara, marayu, da kuma wanda su ke cikin tsananin bukatar kaya, da magani da sauran abubuwa.

Ida ya ce:

"Taimakawa mata da ke fama da cutar VVF a National Obstetric Fistula Centre, Babbar Ruga, Jihar Katsina. Taimakawa wanda suka samu matsalar kwawalwa. Tabbatar da an koyawa matasa dabarun dogaro da kai.
"Taimakawa hukumomi ta duk wata hanya don tabbatar da an kakkabe matsalar shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa.
"Da kuma daukar duk matakin da ya dace don samar da al'umma mai inganci.
"Yau, mun taro don kaddamar da gidauniyar a hukumance. A madadin kwamitin amintattu, muna godiya gareka, sarki, da ka aminta da mu a wannan aikin. Muna tabbatar maka ba zamu fadi ba. Wannan ce masarauta ta farko da ta kaddamar da irin wannan gidauniyar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel