Sarkin Katsina ya nemi alfarma 1 a wajen Shugaba Buhari kafin ya bar Aso Villa

Sarkin Katsina ya nemi alfarma 1 a wajen Shugaba Buhari kafin ya bar Aso Villa

  • Sarkin Katsina ya nemi alfarma a wajen shugaban kasar Najeriya Muhamamadu Buhari
  • Abdulmumini Kabir Usman ya bukaci Gwamnatin Buhari ta kammala ayyukan da aka dauko
  • Mai Martaba ya samu damar yin magana da Muhamamadu Buhari ya kawo masa gaisuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Kafin Muhammadu Buhari ya koma birnin tarayya Abuja, sai da ya tsaya fadar Sarkin Katsina, inda ya yi gaisuwa ga Abdulmumini Kabir Usman.

Rahoton da ya fito daga Katsina Post a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli 2022, ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya kai wa Sarkin Katsina gaisuwar idi.

Da ya mike yana gabatar da jawabi, Mai Martaba Sarki Abdulmumini Kabir Usman ya nemi shugaba Muhammadu Buhari ya karasa ayyukan da ya fara yi.

Sarkin Katsina ya ce daga cikin ayyukan da aka kama hanyar aiwatarwa akwai titin Katsina zuwa Kano, da aikin samar da wuta da ake neman yi a lambar Rimi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Idan an yi nasara wannan dadadden aiki ya soma aiki, jihar za ta samu lantarki daga karfin iska. Rahoton ya ce tun tuni ya kamata a ce an kaddamar da aikin.

Titin dogo zuwa Nijar

Har ila yau, a madadin talakawansa, Sarki ya roki Buhari ya dage wajen ganin an karkare aikin jirgin kasan Kano zuwa Maradi, wanda zai ratsa ta Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar Sarkin Katsina
Muhammadu Buhari da Sarkin Katsina Hoto: @ BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

A jawabinsa, Sarkin ya nuna muhimmancin gwamnatin tarayya ta gama aikin cibiyar binciken ciwon kansa, musamman ganin yadda cutar ke addabar jama’a.

Jaridar ta ce da yake jawabi, Sarkin Katsina ya tabo sha’anin tsaro kamar yadda ya saba, ya nuna har yanzu al’umma su na rayuwa cikin hadari a yankin kasarsa.

Sarki bai kare magana ba sai da ya yabawa gwamnatin Muhammadu Buhari a kan gyara makarantar GCK da ta yi daga matsayin asibitin kwararru.

Kara karanta wannan

Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri

A karshe Abdulmumini Kabir Usman ya yi magana a game da wadanda suka zagaye shugaban kasar.

Masari ya yi wa Buhari rakiya

Mai girma ya je fadar Abdulmumini Kabir Usman ne tare da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da mataimakinsa, Maniru Yakubu da wasu a tawagarsa.

Bayan nan shugaban Najeriyan ya wuce Abuja domin shirin komawa bakin aikinsa.

Tinubu v Kashim

Dazu mu ka ji labari, jam’iyyar APC ta gayyaci Gwamnon, Sanatoci, ‘Yan Majalisa, Ministoci, Shugabanni wajen kaddamar da Kashim Shettima a garin Abuja.

Za a gudanar da bikin kaddamawar ne a dakin taron Shehu Yaradua da aka gina domin tunawa da tsohon 'dan takaran shugaban kasa, Janar Shehu ‘Yar’adua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel