'A Daina Sayen Makamai,' Janar Ya Kawo Dabarar Murƙushe Ƴan Ta'adda cikin Wata 6
- Najeriya za ta iya kawo karshen 'yan ta'adda a cikin watanni shida kacal, a cewar tsohon babban soja, Janar Ishola Williams mai ritaya
- Janar Ishola, wanda ya rike shugaban sashen horo da tsare tsaren tsaron kasa, ya ce Najeriya ba ta bukatar sayen wasu makamai
- A hira da gidan talabijin, tsohon sojan, ya yi bayani dalla dalla kan matakan da ya kamata a dauka don kawo karshen matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban sashen horo da tsare-tsare na hedikwatar tsaro, Janar Ishola Williams (mai ritaya), ya yi bayani kan matsalar tsaro a Najeriya.
Janar Ishola Williams ya bayyana cewa Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin tsaro da take fuskanta cikin watanni shida kacal idan aka sauya salo.

Source: Twitter
Magance matsalolin tsaro a wata 6
Williams ya yi wannan bayani ne a 'shirin hantsi' na tashar Channels TV a ranar Juma’a, inda ya ce babu buƙatar gwamnati ta ci gaba da kashe kuɗaɗe wajen sayen makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Duk waɗannan matsalolin ana iya magance su cikin watanni shida. Abun da ake bukata kawai shi ne a sake fasalin hukumomin tsaro," inji Janar Ishola.
Ya yi watsi da bukatar da kullum kasar ke gabatarwa ta sayo makamai, inda ya ce makaman da ake da su a kasar yanzu haka sun isa a kakkabe 'yan ta'adda da su.
A kan wannan gabar, ya ce:
"A ƙirƙiri sabon tsarin yaƙi mai cike da fasaha, a ƙirƙiri sabon tsarin leƙen asiri da kuma wanda zai kare ƙasar daga masu leƙen asiri, sannan a horar da jami'ai yadda ya kamata.”
Abin da ke sa sojoji tserewa daga sansaninsu
Janar ɗin ya ce akwai bukatar ƙarfafa horo da koyar da sojoji yadda ake yaƙi na gaskiya, saboda da yawa daga cikinsu ba sa fahimtar manufar yaƙin da ake tura su.
Ya yi nuni da cewa:
“Idan ka tambayi soja a Arewa maso Gabas ko Kudu maso Gabas, mecece manufar yaƙin da kuke yi? Ba su sani ba, don ba a taɓa fada musu ba. Don haka idan sun gaji da yakin, sai kawai ka ga suna tserewa idan an farmake su."
Ya ƙara da cewa akwai garuruwa da dama da mutanesu ke bai wa ‘yan ta’adda gagarumar gudunmawa, abin da ke kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati.
Haka kuma, ya soki sarakunan gargajiya da ya ce ba sa taka rawar gani wajen wayar da kan jama’arsu, musamman kan muhimmancin yin aiki tare da hukumomin tsaro.

Source: Twitter
Janar ya ba hukumomin tsaro shawara
Janar Williams ya yi kira ga hukumomin shige da fice, kwastam da ƴan sanda da su yi haɗin gwiwa sosai don hana safarar makamai a kan iyakokin ƙasa.
Ya yi zargin cewa har yanzu ana shigar da makamai ta barauniyar hanya saboda wasu jami’ai na karbar na goro daga masu safarar miyagun makaman.
Rahotanni sun nuna cewa yanzu ƴan ta’adda sun mayar da satar shanu, garkuwa da mutane, da tilastawa manoma biyan haraji a yankunan karkara a matsayin sana’a.
Tinubu na so a magance matsalar tsaro a 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan tsaro, Badaru Abubakar ya ce Shugaba Bola Tinubu ya matsa ƙaimi sai an magance matsalar tsaro a 2025.
Badaru ya bayyana cewa an samu nasara mai girma a ƙoƙarin kakkaɓe duka ƙalubalen tsaron da ake fama da su a sassan Najeriya.
A cewar ministan, shugaban ƙasa Bola Tinubu bai taɓa ƙin amincewa da buƙatar da aka kai masa game da sayo kayan aiki ga sojoji don yaƙar yan ta'adda ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


