Asiri Ya Tonu: An Gano Sabuwar Hanyar da Ake Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya
- Babban hafsan tsaron Najeriya ya ce ‘yan ta’adda sun koma amfani da zinare wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addancin su a kasar
- Janar Christopher Musa ya ce masu daukar nauyin ta’addanci na amfani da hanyoyin batar da kama da taimakon kasashen waje
- Janar Musa ya shawarci ‘yan Najeriya su koyi dabarun faɗa irin su Karate da Taekwondo domin kare kansu daga mugayen mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hedikwatar tsaro ta bankado sabuwar hanyar da 'yan ta'adda ke daukar nauyin ta'addanci a jihohin Najeriya.
Babban hafsan tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa ‘yan ta’adda a sun koma amfani da zinare wajen ɗaukar nauyin ayyukansu.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun koma amfani da zinare
Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke magana a shirin 'Siyasa a Yau' na gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci na bukatar manyan hanyoyin batar da kama, ciki har da tallafi daga kasashen waje.
A cewarsa, irin wannan taimakon da suke samu ne ke ba su damar gudanar da ayyuka ba tare da an iya gano su da wuri ba.
Da aka tambaye shi game da babbar hanyar da 'yan ta'adda ke samun kudaden gudanar da ayyukansu, Janar Chrisopher Musa ya ce:
"Zinare. Suna amfani da zinare wajen gudanar da ayyukansu, wannan ne ya sa yake da muhimmansu gare mu, mu gano hada-hadarsu."
Sabon salon 'yan ta'adda a Najeriya
Game da kokarin da ake yi na ganin an gano masu daukar nauyin ta'addanci a kasar, babban hafsan tsaron ya ce:
"Muna kan bin matakan da suka dace. Dole sai mu cike wasu ka'idoji na doka, kuma saboda abin ya hada da wasu a kasashen waje, wasu kudaden ana shigo da su daga waje, wanda ke zama abin wahala gare mu wajen bin diddiginsu."
Janar Musa ya ce akwai 'yan ta'addan da ke amfani da mutanen gari wajen gudanar da ayyukan ta'addanci.
"Kananun 'yan ta'adda na amfani da mutanen gari ne wajen gudanar da ayyukansu, suna ba su babura, kamar dai an dauke su aiki, sai su rika sanya kudaden a wani asusu."
- Babban hafsan tsaro, Christopher Musa.

Source: Facebook
'"Yan Najeriya su koyi dabarun fada"
Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya shawarci ‘yan Najeriya da su koyi dabarun faɗa domin kare kansu a lokacin haɗari.
Ya ce akwai bukatar mutane su koyi fasahohin faɗa irin su Karate, Taekwondo, Judo da koyon tuƙi, iyo da sauran su.
Janar Musa ya ce ya kamata hukumar NYSC ta rika koyar da ɗaliban da suka kammala karatu dabarun faɗa ba tare da makami ba domin tsira daga mugayen mutane.
Hafsun Najeriya ya yi maganganu kan tsaro
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Janar Christopher Musa ya ce bakin da ke shiga Najeriya suna kara ta’azzarar matsalar tsaro musamman a iyakokin kasar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta
Hafsan tsaron Najeriyar ya bayyana cewa ana sayen makamai cikin sauki a iyaka, yana mai kira a dauki matakai domin kare kasar nan.
Janar Christopher Musa ya ce 'yan ta'addan Boko Haram da Lakurawa sun samu karfi ne bayan an bar su shiga kasar tun farko ba tare da tsangwama ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

