An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano (Hotuna)

An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano (Hotuna)

- Hukumar Hisbah ta Kano tace yanzu jami'an ta zasu iya tunkarar barazanar bata gari

- An karrama babban kwamandan Hisbah saboda yayen bikin horar da jami'an

- Hukumar Hisbah ta Jihar Kano bukaci a horar da karin wasu jami'an

A kalla jami'an Hukumar Hisbah reshan jihar Kano guda 200 ne aka bawa horon kare kai na Kareti kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar Hisbah, Lawal Ibrahim Fagge, shi ne ya bayyana haka ranar Alhamis.

Sanarwar tace babban kwamandan rundunar Hisbah, Harun Ibn-Sina yana cewa jami'an suna ci gaba da daukar horo daban daban don gudanar da aikin su yadda ya dace.

An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano
An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Babban kwamandan, wanda yayi jawabi lokacin da ake mika masa takardar girmamawa da Kungiyar Karetin ta bashi, yace horon zai basu damar kare kansu daga harin bata gari.

An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano
An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya naɗa gwamnan Zamfara sarauta

Da yake magana a wajen horon, an ji kwamandan yana cewa: "Ina ganin irin wannan a talabijin.

"Na zaci abun wasa ne, na zaci abu ne da ake shiryawa saboda shirin Fim sai yau da na gani da idona. Na ga yadda jami'ai na ke fasa bulo da hannu ba tare da sunji ciwo ba. Wannan abin sha'awa ne."

"Jami'an mu a shirye suke da su dinga karbar irin wannan horo don tunkarar duk wani hadari lokacin gabatar da aiki.

"To, irin wannan horo zai taimaka musu don kare kansu in an kawo musu hari," a fadar sa.

An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano
An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

Ibn Sina, ya bukaci wanda suka samu horon da su ci gaba da motsa da jiki da kwada abin da aka koya musu don zama.

An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano
An bawa jami'an Hisbah 200 horon kare kai a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Yayin bikin karramamar Ibn-Sina ya bayyana cewa lambar yabon da aka bashi ba iya shi zata karawa karfin gwiwa ba, hadda ragowar jami'an sa, ya kuma roki da akara daukar wasu jami'an don basu irin wannan horo.

Da ya ke jawabi, shugaban kungiyar karetin, Salisu Ibrahim, wanda aka sani da She-Han, ya bayyana cewa sun bada lambar girma ga shugabancin Hisbah saboda yadda suka taimaka aka harkar ci gaban Kareti a fadin jihar.

A wani labarin, wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu.

Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel