Yadda Sanatoci 109 Ke Cinye Kudin da Za a Iya Biyan Albashin Farfesoshi 4700 a Jami'a
- Rahoto ya nuna cewa sanatocin Najeriya 109 na cinye sama da Naira biliyan 2.354 duk wata, wanda ya isa a biya albashin farfesoshi 4,708
- A baya, an ji cewa Sanata Kawu Sumaila ya ce kowanne sanata yana karɓar kimanin Naira miliyan 21.6 na kuɗin gudanar da ofis a wata
- Abin mamaki, shugaban kungiyar CONUA, Dakta Niyi Sunmonu, ya ce albashin farfesoshi a jami'o'in Najeriya N500,000 ne kacal
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahoto ya nuna cewa ana kashe wa sanatocin Najeriya 109 fiye da Naira biliyan 2.354 a matsayin albashi da kuɗin gudanar da ofis a kowanne wata.
Naira biliyan 2.354 kuwa ta isa a biya albashin farfesoshi 4,708 da ke a jami’o’in Najeriya a kowanne wata, kamar yadda rahoton ya nuna.

Source: Twitter
Matsalar albashi ga farfesoshi a Najeriya
Jaridar Daily Trust dai ta ce har yanzu ana ci gaba da muhawara kan yadda ake ganin rashin daidaito a albashin manyan jami’an siyasa da kuma malaman jami’a.
Kwanan nan kafafen sada zumunta suka cika da labarin Farfesa Nasir Hassan-Wagini na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
Legit Hausa ta rahoto cewa an ga Farfesa Wagini yana sayar da kayan miya da ya noma a kasuwar Batsari, yayin da wasu malaman jami'ar suka koma yin kwadago.
Rahoto ya gano cewa matsakaicin albashin da farfesa a jami'ar Najeriya yake karɓa a wata ba ya wuce ₦500,000, bayan nan a kan cire haraji da wasu rage-rage.
Amma kuma, sanata guda yana karɓar ₦21.6m a matsayin albashi da kuɗin tafiyar da ofis a kowanne wata.
Albashin da sanatoci ke karba duk wata
A ranar 14 ga Agusta, 2024, Sanata Kawu Sumaila (Kano ta Kudu) ya faɗa wa BBC Hausa cewa shi kan sa yana karɓar ₦21.6m a kowane wata – kuɗin da za a iya biyan albashin kusan farfesoshi 43.
Sanata Kawu Sumaila ya ce:
“Kuɗin da ake karɓa na albashi a wata bai kai Naira miliyan ɗaya ba, idan an yi yanke-yanke yakan dawo kamar Naira dubu ɗari shida da ɗan wani abu a matsayin albashi.
“Saboda ƙari da aka samu, a majalisar dattawa ana ba wa kowane sanata Naira miliyan 21 a kowane wata a matsayin kuɗin gudanar da ofis ɗinsa."
Wannan furuci nasa ya biyo bayan ikirarin hukumar RMAFC cewa kowane sanata daga cikin 109 na karɓar jimillar albashi da alawus na ₦1.06m kacal a wata.

Source: Facebook
Albashin da farfesoshi ke karba duk wata
Da yake magana da manema labarai, shugaban ƙungiyar malamai ta CONUA na ƙasa, Dakta Niyi Sunmonu na jami’ar Obafemi Awolowo Ile-Ife, ya ce malamai suna kan tsarin albashi ɗaya tun daga 2009, sai a bara gwamnatin tarayya ta ƙara wa farfesoshi albashi da kaso 35%, sannan 25% ga sauran malamai.
Dakta Niyi Sunmonu ya ce:
“Yanzu haka, babban albashin farfesa bai wuce ₦700,000 ba, bayan an cire haraji da sauran rage-rage, albashin na koma wa kusan ₦500,000.”
Ya tunatar da cewa a shekarun 1960s, bayan Firayim Minista da alƙalan Kotun Ƙoli, farfesoshi ne na uku mafi girman albashi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Duk da sabuwar doka, Katsina da jihohin Arewa 14 sun ki biyan ƴan fansho akalla N32,000
Dakta Niyi ya ce a lokacin su ma farfesoshi, kamar ’yan siyasa suke, domin suna da kuɗin tafiyar da ofis, direba, ma’aikacin gida da akalla yaron ofis guda daya.
Majalisa ta karyata kalaman Kawu Sumaila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar dattawa ta musanta cewa ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi da alawus-alawus duk wata.
Mai magana da yawun majalisar, Adeyemi Adaramodu ya bayyana cewa kudin da Kawu Sumaila ya yi iƙirarin ana ba shi ba albashi ba ne.
Sanata Adeyemi Adaramodu ya yi nuni da cewa Naira miliyan 21 kuɗin gudanarwa ne domin ayyukan ofis inda ya ce albashin sanatocin N1m ne kawai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

