Gyaran Agogo da Sana'o'i 9 da Ke Fuskantar Barazanar Ɓacewa saboda Fasahar Zamani

Gyaran Agogo da Sana'o'i 9 da Ke Fuskantar Barazanar Ɓacewa saboda Fasahar Zamani

  • Fasahar zamani sun rusa sana’o’in gargajiya da dama, inda yawanci suka rasa armashinsu saboda wayoyin hannu da kuma yanar gizo
  • Sana’o’i kamar sayar da kaset, DVD, gyaran rediyo da agogo, da ɗaukar hoto sun fuskanci koma baya saboda tasirin fasahonin zamani
  • A wannan rahoto, Legit Hausa ta yi bayani game da wasu sana'o'i 10 da suke fuskantar barazanar bacewa saboda sababbin fasahohi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bincike ya bankado yadda fasahar zamani ke canza yanayin sana’o’in gargajiya a Najeriya, inda yawancin sana’o’in da suka dade suna ciyar da iyali ke neman zama tarihi.

A yayin da ci gaban fasaha ke bude sababbin kofofin tattalin arziki, a daya bangaren kuma, ya janyo durkushewar wasu sana'o’in da suka shahara a baya.

Sana'o'i da dama ciki har da saye da sayar da kaset, CD/DVD da gyaran agogo na fuskantar baranazar bacewa saboda zuwan zamani
Masu sayar da littattafai, kaste, gyaran rediyo na fuskantar barazanar bacewa saboda zuwan zamani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Da dama daga cikin masu waɗannan sana’o’in sun tsinci kansu a cikin wani hali na dole su canza sana’a ko kuma su rasa hanyar samun abinci, inji rahoton BBC Hausa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rahoto ya lissafo wasu tsofaffin sana'o’i 10 da suka fuskanci kalubale mai girma saboda zuwan na'urorin zamani da yanar gizo.

1. Sayar da kaset

Sana'ar sayar da kaset ta durkushe saboda zuwan mp3 da wayoyin zamani
Sana'ar sayar da kaset ta durkushe saboda zuwan mp3 da wayoyin zamani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wani lokaci da ya wuce, kaset ya kasance tushen sauraren waƙoƙi, karatuttukan addini, da shirye-shiryen rediyo.

Mutane sukan je shagunan sayar da kaset domin su samu abin sauraro a gida ko cikin mota.

Haka kuma, akwai masu sayar da kaset din da babu komai a ciki, wanda zai ba mutane damar naɗar dukkanin sautikan da suke so.

Sai dai, tare da bullar na'urorin mp3 da kuma wayoyin zamani, wanda kowa ke iya sauke waƙa ko karatun da yake so kai tsaye, kasuwar kaset ta durkushe.

Ana samun masu sayen kaset jefi-jefi, musamman wadanda suke da motocin da rediyonsu na kaset ne.

2. Sayar da DVD/CD

Kasuwar sayar da DVD/CD ta durkushe saboda zuwan YouTube, Netflix da sauransu.
Kasuwar sayar da DVD/CD ta durkushe saboda zuwan YouTube, Netflix da sauransu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan sana'a ta sayar da faya-fayen DVD da CD masu ɗauke da fina-finai ko wakoki na neman zama tarihi a Najeriya da ma duniya baki daya, inji rahoton The Hollywood Reporter.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun titsiye Sarki a dajin Zamfara, ya amsa tambayoyi masu zafi

A baya, dillalan fina-finai da ’yan kasuwa sun dogara kacokam a kan wannan sana’a. Wasu ma sukan buɗe shaguna, suna karbar kuɗi suna ba mutane hayar faya-fayan DVD/CD su kalla.

Amma yanzu, shafukan yanar gizo irin su YouTube, Netflix, da sauransu sun maye gurbin DVD/CD, inda mutane ke kallon fina-finai kai tsaye a wayoyinsu ba tare da siyan faya fayen ba.

Ana samun masu sayen CD jefi-jefi, musamman wadanda suke da motocin da rediyonsu na CD ne.

3. Gyara da sayar da rediyo

Sana'ar gyara da sayar da rediyo ta durkushe saboda zuwan wayoyin hannu
Sana'ar gyara da sayar da rediyo ta durkushe saboda zuwan wayoyin hannu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A lokutan da suka shude, rediyo ya kasance wani muhimmiyar na’ura da za a same ta a kusan kowane gida a Najeriya. Ya kasance abokin hira, mai kawo labarai da nishadi.

Wannan ya sa kasuwar sayar da shi da na gyaransa suka habaka matuka, inda za ka iya ganin masu gyara ko sayar da rediyo a cikin kusan kowace anguwa da kasuwa.

Amma a yanzu, da yake kusan kowace waya ta zamani tana da manhajar rediyo, mutane sun janye daga sayen rediyon gargajiya.

Wannan ya yi mummunan tasiri ga masu gyara da sayar da rediyo, inda suka rasa hanyar da suka dade suna samun rufin asiri da ita.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

4. Gyara da sayar da agogo

Yanzu kasuwar gyaran agogo ta tumu, yayin da aka rage sayen agogon hannu da na bango saboda wayoyin hannu.
Kasuwar gyaran agogo ta tumu, yayin da aka rage sayen agogon hannu da na bango saboda wayoyin hannu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A baya mutane da dama sukan sanya agogon hannu don duba lokaci da kuma ado wanda ya sanya kasuwar gyaran agogo ta yi fice sosai.

Sai dai, kasancewar kowace wayar hannu tana da agogo, mutane sun daina damuwa da sanya agogon hannu. Har ma amfani da agogon bango ya ragu sosai.

Wannan ya sa masu gyaran agogo suka rasa kwastomomi. Duk da cewa har yanzu ana yin agoguna na zamani, amma ba kowa ke da fasahar gyara su ba.

5. Sayar da fitila da gyara ta

Zuwan fitulu masu amfani da cajin wutar lantarki da hasken rana, kasuwar fitun kwai da cocilar batir ta mutu.
Zuwan fitulu masu amfani da cajin wutar lantarki da hasken rana, kasuwar fitun kwai da cocilar batir ta mutu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A kauyukan da babu wutar lantarki, ko kuma a biranen da aka dauke wutar, to fitilar kananzir ko fitilar batir ita ce mafita ga kowa wajen ganin haske.

Saboda haka, sayarwa da gyaranta sun kasance sana'o’i masu riba a baya.

Amma yanzu, fitilu masu caji da wutar lantarki, fitilu masu caji da hasken rana, da kuma hasken waya mai karfi sun maye gurbin waɗannan fitilu na gargajiya, wanda ya sa sana'arsu ta daina armashi gaba daya.

Kara karanta wannan

Shugabanin ADC a jihohi sun shirya tumbotsai, za su jawo matsala ga tafiyar 2027

6. Sayar da katin waya

Saboda sayen katin waya a banki, POS da manhajojin sayar da katin, ya sa kasuwar katin waya ta takarda ta mutu.
Saboda sayen katin waya a banki, POS da manhajojin sayar da katin, ya sa kasuwar katin waya ta takarda ta mutu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A shekarun baya, shagunan sayar da katin waya sukan cika da jama’a masu sayen kati don yin kira ko aika saƙonni a wayoyinsu.

Amma yanzu, fasahar zamani ta kawo manhajojin bankuna, wuraren cirar kudi na POS, da kuma manhajojin sayan kati a waya, wanda ya sauya tsarin katin takarda.

Jaridar The Sun ta rahoto cewa yawancin mutane sun daina sayen katin waya na takarda daga shaguna, wanda hakan ke barazana ga rayuwar masu sana'ar sayar da kati.

7. Janyewar sana'ar ɗauka da wanke hoto

Wayoyin hannu masu karfin kyamara sun kashe kasuwar daukar hoto ta studio.
Wayoyin hannu masu karfin kyamara sun kashe kasuwar daukar hoto ta studio. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A da, idan mutum yana son ɗaukar hoton fasfo ko hoton wani taro, sai ya je dakin daukar hoto da ake kira da studio a turance.

A kan dauki hoton da kyamara, sannan a je dakin duhu, a wanke hoton kafin a ba mutum shi, wanda kan dauki awanni ko kwanaki.

A yanzu, duk da ci gaban da ake samu a sana’ar, fasahar wayoyin zamani masu kyamarar da ke da inganci sosai sun rage buƙatar zuwa dakunan daukar hoto.

Kara karanta wannan

Tsofaffin sojojin Najeriya sun fara zanga zanga, sun mamaye ofishin ministan kuɗi

Wayoyin zamani ma suna da manhajojin gyaran hoto, har da waɗanda ke iya ɗaukar hoton fasfo, kuma ba sa bukatar sai an wanke hoton kati.

8. Janyewar sana'ar sayar da littattafai

Zuwan PDF, e-book da wayoyin hannu da kwamfuta, an juyawa kasuwar sayar da littattafai baya
Zuwan PDF, e-book da wayoyin hannu da kwamfuta, an juyawa kasuwar sayar da littattafai baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shagunan sayar da littattafai sun yi fice a baya, musamman idan aka ce shagunan na a kusa da makarantu.

Daliban makaranta, malamai, da sauran jama’a suna sayen littattafan karatu da na addini a wajen masu sayarwa.

Amma yanzu, saboda zuwan manhajojin karatu, e-books da kuma littattafan PDF, mutane na sauke duk wani littafi da suke buƙata a waya ko kwamfuta, hakan ya sa kasuwar littattafan takarda ta ja baya.

Duk da hakan, har yanzu ana sayar da littafai a manyan kasuwanni, makarantu da shaguna, saboda akwai karatuttukan da dole sai a littafin za a yi shi.

9. Sana'ar aika saƙo/kiran waya

Bayan wadatar wayoyin hannu da zuwan Facebook, WhatsApp, kasuwar buga waya da aika sako ta mutu
Bayan wadatar wayoyin hannu da zuwan Facebook, WhatsApp, kasuwar buga waya da aika sako ta mutu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sana’ar kiran waya ta kasance wata babbar hanyar sadarwa a shekarun baya ga waɗanda ba su mallaki waya ba.

Idan mutum na son yin kira ko aika saƙo, to dole sai ya je shagon kiran waya ya biya kuɗi, inda za a caje shi a kan kowane minti ko ko duk sako daya.

Kara karanta wannan

Dangote ya bude wa 'yan Najeriya guraben neman aiki a kamfaninsa

Amma yanzu, wayoyin hannu sun yadu a ko’ina, kuma akwai manhajojin kira da aika sako kyauta na WhatsApp, Facebook da Instagram da sauran su, wadanda suka sa shagunan kiran waya suka zamo tarihi.

10. Sayar da waƙoƙi ta bluetooth

Kasuwar sayar da wakoki ta bluetooth ta durkushe bayan zuwan su Boomplay, Spotify, AudioMack.
Kasuwar sayar da wakoki ta bluetooth ta durkushe bayan zuwan su Boomplay, Spotify, AudioMack. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A shekarun baya, matasa sukan je wurin masu sayar da waƙoƙi a shaguna don a tura musu waƙoƙi ta hanyar Bluetooth ko kuma a tura musu a katin fasaha na M-Card ko kaset.

Yanzu da zuwan yanar gizo da manhajoji irinsu Boomplay, Spotify, da AudioMack, kowa zai iya sauke waƙar da yake so a wayarsa, wanda hakan ya kashe wannan sana’ar gaba daya.

"Ni tuni na canja sana'a" - Abdulkarim Bauchi

Legit Hausa ta ji ta bakin Malam Abdulkarim Bauchi, wanda ya gaji sana'ar mahaifinsa ta gyaran rediyo kan kalubalen da sana'arsu ke fuskanta yanzu.

Malam Abdulkarim ya ce tuni ya daina wannan sana'ar, ya koma sana'ar gyaran Talabijin, duk da a cewarsa, ita ma ba wani ci take yi sosai ba.

"Ai Malam Sani na dade da daina wannan sana'a, kusan shekaru 10 kenan. A haka ma wasu na ganin na jure sosai da na ci gaba da sana'ar saboda an daina yayin rediyo yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun harbe 'dan limamin Abuja, ya mutu har lahira

"Mafi akasarin masu amfani da rediyo dattawa ne, su din kuma sukan jima ba ta lalace ba saboda ba yawo ake da ita ba, kullum tana ajiye a waje daya.
"Yanzu na rungumi sana'ar gyaran talabijin, kasan fasahar gyaran nasu ba wani bambanci ne sosai ba, don haka sai na je na yi wata shida na fahimci sana'ar sannan na fara."

Malam Abdulkarim ya ce a wajen mahaifinsa, Liman Abdallah Bushara ne ya koyi sana'ar, tun lokacin suna zaune a anguwar Lushi da ke karamar hukumar Bauchi.

"Ina lallabawa, amma babu kasuwar" - Madam Ramatu

A bangaren sayar da katin waya, Legit Hausa ta tuntubi Madam Ramatu da ke sayar da katin waya a yankin Bakin Ruwa, Kasuwar Bacchi da kewayen Rigasa game da kasuwar a yanzu.

"Gaskiya yanzu kasuwar kati ta yi kasa sosai, amma har yanzu ana bugawa kuma muna rabawa, sai dai ba kamar yadda ka sani a shekaru biyar baya ba.
"A 2020, ina iya sayar da katin waya na sama da N700,000 a rana daya kawai, saboda ina raba ma sama da shaguna 30 a tsakanin Rigasa, Bakin Ruwa da Kasuwar Bacci, da wasu anguwanni, irin su Unguwar Sanusi.

Kara karanta wannan

Mutanen gari da 'yan sanda sun yi arangama da 'yan sanda a Abuja, an samu asarar rai

"Amma yanzu, da kyar ake iya sayar da na N150,000 zuwa N200,000. Masu shagunan sun daina saya, sun ce su ma ba a saya, kowa ya saba da sanya kati daga wayarsa."

Wayar zamani ta gaje komai

A taƙaice, waɗannan sana’o’i 10 sun fuskanci durkushewa ne saboda wayar zamani ta gaje su. A halin yanzu, waya ce ginshikin rayuwar mutane.

Ana amfani da waya wajen yin hada hadar banki, siya da sayarwa, karatu, sadarwa, kallo, da dai sauransu.

Wannan babban sauyi ya rage dogaro da ayyukan da ke buƙatar hulɗa kai tsaye, wanda ya nuna yadda waya ta zama cibiyar rayuwar yau da kullum kuma ta canza rayuwar mutane gaba daya.

Amfanin koyon sana'o'in hannu ga matasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, da yawa daga cikin masu sana'o'in hannu su kan samu kwanciyar hankali gami da arziki fiye da samun masu aikin gwamnati.

An ji cewa yin sana'ar hannu wata hanya ce ta yakar talauci da kuma yunwa duk da wasu na ganin cewa sana'ar hannu ba ta kawo dukiya mai tarin yawa lokaci guda.

Sana'ar hannu tana koyawa mutane kawar da kai daga abun hannun mutane domin tana cire munanan sake-sake a zuciya da ke kai ga aikata miyagun ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com