Dogaro da kai da sauran dalilai 4 da ya kamata mutum ya koyi sana'ar hannu

Dogaro da kai da sauran dalilai 4 da ya kamata mutum ya koyi sana'ar hannu

A wani lokacin ana alakanta muhimmancin koyon sana'ar hannu tamkar yadda ruwa ke da muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Tabbas hakan take kuwa domin rayuwa ba za ta taba tafiya daidai ba ga wanda ba ya da abun yi ba.

Da yawa daga cikin masu sana'o'in hannu su kan samu kwanciyar hankali gami da arziki fiye da samun masu aikin gwamnati ko kuma masu aiki a wurare masu zaman kansa.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu dalilai shida da suka dace mutum ya koyi sana'ar hannu duba da muhimmancin hakan da a halin yanzu ya zamto gishirin zaman duniya.

1. Yakar tsumangiyar kan hanya wato yunwa da kuma talauci:

Mai sana'ar hannu ba ya da wani tashin hankali a yayin da yunwa ta tasar masa wata bukata ta rayuwa. Yin sana'ar hannu wanta hanya ce ta yakar talauci da kuma yunwa. Sai dai wasu masu karancin fahimta da kuma rashin hangen nesa, na ganin cewa sana'ar hannu ba ta kawo dukiya mai tarin amma kuwa hausawa na cewa da babu gwara babu dadi. Hakazalika tsumangiyar kan hanya wato yunwa hausawa na yi mata kirari na cewar babu ruwan ta da girma ko kankantar mutum, kowa ta samu sai ta fyade.

2. Samuwar aiki ko kuma abun yi:

Duk da cewa komai rabo ne kuma komai da lokacinsa, samun aiki ya yiwa hakar zinare fintinkau ta fuskar wahala da kuma tsanani a Najeriya. Wannan dalili ya sanya masu sana'ar hannu ke zaune cikin kwanciyar hankali ta samun abun yi da kuma rashin fargaba ta rashin aiki.

3. Dogaro da kai da rashin hangen na wani:

Mutane da dama masu sana'ar hannu su kan dogara da kawunansu wajen biyan bukatu. Tabbas masu sana'ar hannu babu ruwansu da dogaro a kan wasu mutanen wajen neman samun biyan bukatun su na rayuwar yau da kullum. Sana'ar hannu ta horarsa da masu ita ga kawar da kai daga abun hannun mutane.

4. Rage aukuwar laifuka:

Sana'ar hannu tana koyawa mutane kawar da kai daga abun hannun mutane. Shakka babu rashin abun yi ya kan haifar da munanan sake-sake a zuciyar mutane. Wannan lamari ya kan jefa su cikin aikata miyagun laifuka domin samun na batarwa kamar yadda take kasancewa a Najeriya.

KARANTA KUMA: Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

Kasar Najeriya kamar yadda wasu masu sharhi suka bayyana na fama da ta'addancin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a sakamakon talauci da ya yiwa mafi rinjayen kaso na al'ummar kasar.

5. Bude kofofin samu:

Har ta ga masu aikin gwamnati ko kuma a wasu wurare masu zaman kansu, masu hada sana'ar hannu da kuma aiki a lokaci guda su kan samu yalwar arziki fiye da wadanda ba suyi riko da ita ba.

An shawarci masu aiki da su koyi sana'ar hannu ko kuma kafa wasu harkokin kasuwanci da zasu dogara a kai a yayin barin aiki domin kuwa rayuwa ba ta da tabbas.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel