Dr Osei Kwame: Mutumin da ya zama hamshakin miloniya da sana'ar sayar da kaset

Dr Osei Kwame: Mutumin da ya zama hamshakin miloniya da sana'ar sayar da kaset

- Dr. Osei Kwame Despite shine shugaban kamfanin Despite Group of companies

- Ya fara ne daga karamin dan kasuwa mai siyar da kasusuwa, makulli, abin shayar da jarirai da sauransu inda a yanzu ya zama babban miloniya

- YEN.com.gh ta bayyana manyan kasuwancin babban dan kasuwar kasar Ghana din

Dan kasuwar kasar Ghana kuma sananne a harkar yada labarai, Osei Kwame Dsepite na daya daga cikin ‘yan kasuwar kasar Ghana masu tarin nasara a kasuwancinsu.

An haifeshi a ranar 2 ga watan Fabrairu 1962. Despite ya fuskanci tarin matsaloli a yayin da yake karami saboda gidansu babu kudi ko wani rufin asiri.

Osei Kwame Despite yayi rayuwa ne kamar yadda kowanne dan talaka yake yi. Ya fara ne da siyar da kasusuwa, makullai da sauran abubuwan bukata a Dunkwa-Offinso.

Dr Osei Kwame: Mutumin da ya zama hamshakin miloniya da sana'ar sayar da kaset
Dr Osei Kwame: Mutumin da ya zama hamshakin miloniya da sana'ar sayar da kaset
Asali: Facebook

Dan asalin Agona Wiamoase din da ke yankin Ashanti na kasar yayi kokarin barin kasarshi inda ya dawo Najeriya don neman arziki.

Amma kuma mafarkin shi na samun dukiya a kasar da ba tashi ba ya datse bayan an mayar da sama da ‘yan kasar Ghana miliyan daya zuwa kasarsu sakamakon umarnin fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Abdulhakim Bashir: Matashin da ya kirkiri fasahar da take kama barayi

Despite ya fara kasuwancin kwangilar itace amma hakan ya tsaya ne bayan da wata bishiya ta fado ta lalata mishi injin kayar da bishiyar.

Osie Kwame ya jajirce inda ya koma sana’ar kayayyaki bayan ya bude shago tare da fara kasuwancin shi a cikin kasar shi. Daga nan ne fa arziki ya bude har ya kafa kamfanin Despite Group of Companies, wanda yake daya daga cikin manyan kamfanonin kasar Ghana.

Kamfanin ya mayar da hankali ne wajen samar da kayan abinci, kayan shayi, hako ma’adanai, dillancin gidaje, kafar yada labarai da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng