Abinda ya sa na garkame shagon daukar hoton Sani Danja a Kano - Afakallahu

Abinda ya sa na garkame shagon daukar hoton Sani Danja a Kano - Afakallahu

- Hukumar tace fina-finai da dabi’a ta jihar Kano ta yi karin bayani a kan dalilan da yasa ta rufe wasu wuraren nishadantarwa a jihar

- Shugaban hukumar, Isma’’ila Na’abba Afakallahu ya musanta zargin da jama’a suke musu na cewa ba hakkinsu bane kula da dakunan daukar hoto

- Ya ce duk abinda ya shafi hoto mai motsi ko mara motsi na karkashinsu har da dakunan shan magani na Musulunci

Shugaban hukumar tace fina-finai da dabi’a ta jihar kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallahu) ya bayyana cewa hukuma sa ta kulle shagon daukar hoto na ‘celebrity Photography’, mallakar jarumi Sani Danja ne saboda ya na cikin aikin hukumar ta su.

Afakallahu yayi bayanin ne bayan cece-kucen da ya barke, musamman a Kannywood game da wata rundunar aiki da ya kafa domin kula da wasu sana’o’i a jihar. A cikin sana’o’in kuwa har da daukar hoto da saida magungunan Musulunci wato Islamic Chemist.

A ranar Litinin 27 ga watan Janairu 2020 ne Afakallahu ya kafa wannan tawagar aikin mai taken ‘Idan baka yi, bani wuri’, kamar yadda jaridar Fim Magazine ta ruwaito.

Kamar yadda hukumar ta bayyanawa manema labarai, ayyukan wannan tawagar ya hada da tantancewa da tsaftace dukkan wani abu da ya shafi nishadantarwa.

KU KARANTA: Tashin hankali: Ladani ya bawa makwabcinsa zakami ya sha ya mutu

“Sai dai kuma duk wanda ke sana’ar nishadi ba tare da lasisin tabbatar da inganci ba, wannan tawagar za ta kama tare da kulle masana’antar shi kuma ta gurfanar da shi,” in ji jami’in yada labaran hukumar, Mal. Salihu Adamu Aliyu.

A ranar 3 ga watan Fabrairu ne tawagar ta fara aikinta inda ta fara da garkame shagon daukar hoto na jarumi Sani Danja. Mutane da yawa sun ce hukumar ba ta da alaka da wajen daukar hoto ko kuma Islamic Chemist.

Amma Afakallahu ya ce “hukumar na kula tare da tantance duk wani hoto mai motsi da mara motsi. Ganin harkokin fim ne suka danne sauran harkokin. Dole ne mu dinga bincikar hatta dakunan daukar hotunan don mu san me suke ciki. Rashin lasisinmu ne yasa muka rufe su.”

A watannin da suka gabata an kama shugaban hukumar tace fina-finan ya saka an kama jarumai da daraktoci na masana'antar da yawa, inda hakan ya jawo matukar kace-nace a kafafen sada zumunta

Wasu na ganin cew hakan yana da nasaba da jaruman basu goyon bayan gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, gannin cewa mafi akasarin jaruman da aka kama din 'yan Kwankwasiyya ne, wadanda suka nuna goyon bayan su ga dan takarar gwamnan a jam'iyyar PDP, wato Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng