Tattalin Arziki: Sana'o'in da ke kawo kudi da wuri, wadanda basu bukatar babban jari

Tattalin Arziki: Sana'o'in da ke kawo kudi da wuri, wadanda basu bukatar babban jari

Da yawa mutane kan kwanta suna jiran arziki, bayan arziki sai da dabara ake nemo shi, wannan tsokaci ne na irin yadda za'a iya fara sana'a da kudade kadan, musamman ga mata masu zaman gida, da dogaro da me miji ya fita ya kawo.

Sanaoi da mace zata iya daga gida, da jari kadan sun hada da:

1. Sayar da ruwan sanyi, kankara, lamurje, kunun zaki, ko shayi ga masu bukata.

2. Girki, na tuwo, dumame, dafa duka, kayan ganye, ko tafashen nama, ga masu bukata a waje.

3. Sayar da katin waya, ko katin talabijin.

4. Sayar da kayan masarufi, kamar mai, na kuli ko na ja, maggi, kubewa ko kuka, daddawa, da dai kayan zaqaqa miya.

Tattalin Arziki: Sana'o'in da ke kawo kudi da wuri, wadanda basu bukatar babban jari
Tattalin Arziki: Sana'o'in da ke kawo kudi da wuri, wadanda basu bukatar babban jari

5. Dinki, saqa, ko gyaran tsumma na yagaggun kayan yara.

6. Wanki da guga, inda mace kan tara kudin adashi ta ssayi injin wanki ta yi domin lada.

7. Kiwo, na kaji ko na tsuntsaye, har ma da na sauran dabbobi kamar kifi.

8. Karantarwa, dan soro ya isa a tara yara a koya musu ABCD iyayensu kuma su biya, musamman inda babu makarantu sosai. Wannan yakan habaka a hankali ya zama makaranta.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji Aso Rock

9. Sayar da kayan kamshi, ko kuma hada su, ko koyar da hada wa, da ma kayan kwalliyar mata, kamar su lalle da halawa.

10. Yi tunanin sana'a ta 10 wadda bata kawo wahala ko neman babban jari, wadda kuma mata zasu iya yi, iyar da sakon ga masu sauraro ko karatu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng