2027: Malamin Addini Ya Kada Hantar Gwamnoni kan Hadakar Jam'iyyar ADC

2027: Malamin Addini Ya Kada Hantar Gwamnoni kan Hadakar Jam'iyyar ADC

  • Shugaban cocin INRi Evangelical Spiritual, ya hango barazanar da jam'iyyar ADC za ta yi wa wasu gwamnonin Najeriya
  • Primate Ayodele ya bayyana cewa jam'iyyar ADC za ta iya kifar da wasu gwamnoni a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Malamin addinin Kiristan ya nuna cewa wadannan gwamnonin za su iya lashe zabe ne kawai idan suka tafka magudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi wasu gwamnonin Najeriya kan jam'iyyar ADC.

Primate Ayodele ya bayyana cewa jam'iyyar hadaka watau ADC na iya kifar da su a zaɓen shekarar 2027 idan ba su ɗauki matakan kariya ba.

Primate Ayodele ja kunnen gwamnoni
Primate Ayodele ya ce ADC za ta iya kayar da wasu gwamnoni Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Twitter

Malamin addinin Kiristan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin kafafen yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

2027: Yadda aka samu shugabanni 2 ko fiye a ADC da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me malamin addinin ya ce kan gwamnoni?

A cewar Primate Ayodele, wasu daga cikin gwamnonin za su fuskanci ƙalubale wajen sake lashe zaɓe a kujerunsu matuƙar ba su tafka maguɗi ba.

Primate Ayodele ya bayyana cewa jam'iyyar ADC na da ƙarfin kwace wasu kujeru a Najeriya, kuma dole ne gwamnonin su yi aiki tukuru domin su iya ci gaba da riƙe jihohin su.

Limamin Kiristan ya bayyana a fili cewa wasu gwamnonin ba za su iya samun nasarar sake zaɓe a 2027 ba sai ta hanyar maguɗi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

“Wasu gwamnonin Najeriya za su rasa kujerunsu sakamakon ADC idan ba su yi hattara ba; za su samu wahalar samun nasarar sake takara a kujerunsu."
"A zaɓe na gaskiya da adalci, ba za su yi nasara ba; hanyar da za su bi ita ce ta tafka maguɗi."
"Ya kamata su daina raina wannan hadakar; ba lallai ba ne su gane hakan a yanzu, amma dole ne su yi taka-tsantsan sosai."

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

- Primate Elijah Ayodele

Idan ba a manta ba dai, Primate Ayodele ya yi wa wasu gwamnonin jihohi gargaɗi dangane da shirin sake takararsu, inda ya ce tazarcensu bai da tabbas, sai sun tashi tsaye wajen yin addu’a domin samun nasara.

Primate Ayodele ya aika sako ga gwamnoni
Primate Ayodele ya ce ADC za ta kayar da wasu gwamnoni Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Facebook

Karanta wasu karin labaran kan jam'iyyar ADC

Primate Ayodele ya ja kunnen Sanusi II

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya aika da sakon gargadi ga Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Primate Ayodele ya bukaci Mai martaba Sanusi II kan ya bi a hankali sannan kuma ya yi taka tsan-tsan.

Malamin addinin ya yi kira ga Sanusi kan ya sanya lura kuma ya yi taka tsan-tsan musamman kan abin da yake sha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng