Ta Faru Ta Kare, Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Kinkimo Bashin Naira Tiriliyan 32.2

Ta Faru Ta Kare, Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Kinkimo Bashin Naira Tiriliyan 32.2

  • Majalisar Dattawa ta amince da shirin Shugaba Tinubu na karɓo bashi daga waje da cikin gida domin cika kasafin kuɗin shekarar 2025 gaba ɗaya
  • Kwamitocin majalisa sun ce yawancin bukatun bashin sun riga sun shiga kasafin kuɗi kuma za a biya su cikin shekaru 20 zuwa 35 nan gaba
  • Wasu Sanatoci sun bayyana damuwa kan gaskiyar bashin, inda suka ce al'umma na da haƙƙin sanin adadin da kuma yadda za a yi amfani da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – A ranar Talata, majalisar dattawa ta amince da bukatar karɓo sabon bashi daga ƙasashen waje da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar mata.

Shugaba Tinubu ya nemi majalisar ta amince masa ya kinkimo bashin $21bn (Naira tiriliyan 32.2) domin aiwatar da kasafin kuɗi na shekarar 2025.

Kara karanta wannan

An zargi gwamnati da hannu a watsar da aikin titin Kano zuwa Katsina, ana asarar rayuka

Majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu na karbo bashin dala biliyan 21 daga kasashen waje
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana jawabi gaban zaman hadin gwiwar majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Majalisa ta amince Tinubu ya ranto $21.19bn

Jaridar Punch ta rahoto cewa shirin rancen ya haɗa da dala biliyan 21.19 a matsayin rancen kai tsaye da za a karbo daga ƙasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya hada da Yuro biliyan hudu, Yen biliyan 15, da kuma tallafin dala miliyan 65 da take fatan samu.

Harilayau, akwai shirin karbo bashi a cikin gida ta hanyar sayar da takardun lamuni na gwamnati da suka kai Naira biliyan 757.

Majalisar ta kuma amince da karbo karin bashi na dala biliyan biyu ta sabuwar hanyar tara kuɗi da aka tanada da za a fitar da ita a kasuwar kuɗin ketare.

An tsara yadda za a aiwatar da kasafin 2025

Majalisar ta amince da bukatar ne bayan gabatar da rahoton shugaban kwamitin majalisar kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako.

Kwamitin ya bayyana cewa an gabatar da bukatar karɓar bashin zuwa majalisa tun 27 ga Mayu, 2025 amma hutun majalisar da matsalolin takardu daga ofishin DMO ya kawo tsaikon gabatar da rahoton.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi bayani yayin da aka fara taron daidaita farashin fetur a Abuja

Shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawa, Sanata Olamilekan Adeola, ya bayyana cewa tuni aka cimma yawancin bukatun bashin cikin tsarin tsare-tsaren kuɗi na dogon lokaci (MTTF) da kuma kasafin 2025.

Yayin da yawancin Sanatoci suka goyi bayan shirin, wasu sun bayyana damuwa dangane da gaskiya da kuma yadda za a yi amfani da bashin.

Majalisar dattawa ta ce za a yi amfani da kudin ne wajen aiwatar da kasafin 2025-2026
Zauren majalisar dattawan Najeriya da ke babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Martanin sanatoci kan karbo bashin $21bn

Sanata Sani Musa ya fayyace cewa ba za a fitar da bashin gaba ɗaya a 2025 ba, illa dai a rarraba shi cikin shekaru shida, yana mai cewa hakan bai saba da dokokin tattalin arzikin duniya ba.

“Babu wata ƙasa da ke bunƙasa ba tare da karɓar bashi ba. Wannan matakin ya yi daidai da abin da ake yi a duniya,” a cewar Sanata Sani Musa.

Sanata Adetokunbo Abiru, shugaban kwamitin harkokin banki da inshora, ya tabbatar wa da majalisar cewa bashin yana da sauƙin biya.

“Wadannan basussukan na dogon lokaci ne, don wasu za a biya ne a shekara 20 zuwa 35, kuma an dabaibaye su da muhimman ayyukan raya kasa da ci gaban ɗan adam."

- Sanata Adetokunbo Abiru.

Kara karanta wannan

Ana rade radin zai shiga jam'iyyar APC, an hango Kwankwaso a fadar shugaban kasa

Amma Sanata Abdul Ningi ya bayyana damuwa kan yadda za a tsage gaskiya game da bashin, yana mai cewa ‘yan Najeriya na da haƙƙin sanin adadin bashin da kuma inda za a yi amfani da su.

“Ya kamata mu faɗa wa al’ummarmu adadin bashin da ake karbowa a madadinsu, da kuma dalilin da yasa ake karbo su,” a cewar Sanata Ningi.

Tinubu na so majalisa ta amince ya karbo bashi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya tura wasiƙa zuwa majalisar wakilai yana neman amincewa da shirin karɓo bashin $21.5bn daga ƙasashen waje.

Ya kuma nemi izini don ɗaukar bashin cikin gida na ₦757.9bn da za a yi amfani da shi wajen biyan bashin fansho da ake bin gwamnati.

A cewarsa, bashin zai taimaka wajen cike gibi a kuɗaɗen shiga da kuma gina tubalin ci gaba, musamman bayan cire tallafin mai daga kasafin gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com