Mu na so ayi wa mutanen Najeriya bayanin bashin da gwamnati ta karbo – SERAP

Mu na so ayi wa mutanen Najeriya bayanin bashin da gwamnati ta karbo – SERAP

Wata kungiya mai yaki da rashin gaskiya, SERAP, ta maka gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kotu kan gazawarta na yin bayani game da bashin da ta ke karbowa.

Wannan kungiya ta SERAP ta na so gwamnatin tarayya ta rika yi wa ‘Yan Najeriya bayani dalla-dalla game da kudin da ta aro daga kasar waje tun daga lokacin da ta karbi mulki.

SERAP ta fitar da jawabi a shafinta na Twitter ta na cewa: “Mun bukaci babban kotun tarayya da ke garin Abuja ta tursasawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi cikakken bayani game da bashin kudin da gwamnatin ta karbo tun daga Mayun 2015.”

Kungiyar ta na son sanin ruwan da bashin da wannan gwamnati ta ke karbowa su ke dauke da su. Haka kuma ta nemi sanin adadin kudin da Najeriya ta aro da yadda aka kashe su.

A wannan kara mai lamba ta FHC/ABJ/CS/785/2020 da aka shigar a gaban kotu a makon jiya, SERAP ta nemi Alkali ya umarci gwamnatin APC ta bayyana sharudan bashin da ta karbo.

KU KARANTA: Kungiyoyi su na so a binciki Ministan shari'a a Najeriya

Mu na so ayi wa mutanen Najeriya bayanin bashin da gwamnati ta karbo – SERAP
Ministar kudi, Zainab Ahmed
Asali: Depositphotos

Fitowa ayi wa jama’a bayani zai taimaka wajen ganin cewa ba a karkatar da wannan kudi da aka karbo a matsayin bashi zuwa aljihun tsirarun jami’an gwamnati ba inji SERAP.

Yin hakan zai kuma kara kwantar da hankalin mutanen kasar cewa bashin da aka karbo zai yi masu amfani, tare da gamsar da wadanda su ka ba Najeriya aron wadannan kudi.

Karar da SERAP ta shigar ya dogara ne da dokar FOI da ta ba ‘yan kasa samun bayanan gwamnati. Wannan ya na kuma cikin kudirorin majalisar dinkin Duniya na yaki da barna.

Mataimakin darektan kungiyar SERAP, Kolawole Oludare, ya bayyana cewa su na karar har da ministocin kudi da na shari’an Najeriya; Zainab Ahmed da Abubakar Malami.

Har ila yau, kungiyar mai zaman kanta, ta na tuhumar shugabar hukumar DMO da ke kula da bashin Najeriya. Za a tursasa wadannan jami’ai su fitar da bayanan da ake bukata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel