Jerin kasashe 25 da suke da karfin tattalin arziki a duniya
Ana tantance karfin tattalin arzikin kasashe ne ta hanyar cigaban da suke samu ta hanyar kasuwanci, da kuma yawan jarin da kasar ta ke da shi, da kuma tasirin da tattalin arzikin ya ke da shi ga al'ummar da ke zaune a wadannan kasashe
Hakan ne ya sanya ake amfani da tattalin arzikin kasashe wurin tantance kasar da ke da arziki da kuma wacce ta ke fama da talauci.
Fitar da kaya zuwa wasu kasashe ba karamin muhimmanci ne da shi ba ga bunkasar tattalin arzikin kasa da kuma kayyade karfin tattalin arzikin kasashe.
Majiyarmu LEGIT.NG ta binciko muku jerin kasashe 25 da suke da karfin tattalin arziki a duniya, kasar China, Amurka da kasar Jamus sune manyan kasashen duniya guda uku da suke da karfin tattalin arziki a bangaren kasuwanci.
KU KARANTA: Wani mutumi ya saki matarshi kwana daya bayan daurin aurensu
Ga jerin kasashen duniyar a kasa da kuma yawan jarin da suke dashi na kasuwanci:
Kasa Yawan Jari
1. China $ 1,990,000,000,000
2. Amurka $ 1,456,000,000,000
3. Germany $ 1,322,000,000,000
4. Japan $ 634,900,000,000
5. South Korea $ 511,800,000,000
6. France $ 507,000,000,000
7. Hong Kong $ 502,500,000,000
8. Netherlands $ 495,400,000,000
9. Italy $ 454,100,000,000
10. UK $ 407,300,000,000
11. Canada $ 393,500,000,000
12. Mexico $ 374,300,000,000
13. Singapore $ 361,600,000,000
14. Switzerland $ 318,100,000,000
15. Taiwan $ 310,400,000,000
16. Dubai $ 298,600,000,000
17. Russia $ 281,900,000,000
18. Spain $ 280,500,000,000
19. Belgium $ 277,700,000,000
20. India $ 268,600,000,000
21. Thailand $ 214,300,000,000
22. Ireland $ 206,000,000,000
23. Poland $ 195,700,000,000
24. Australia $ 191,700,000,000
25. Brazil $ 184,500,000,000
Hakazalika, majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton jerin kasashe 10 da suka fi kowacce kasa arziki a duniya a wannan shekarar ta 2019.
Wani abun mamaki shi ne, kasashen da suke da arzikin sune kasashen da basu da girman a duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng