Wata Sabuwa: ASUU Ta Hana Malamai Shiga Aji a ATBU da Wasu Jami'o'i, An Ji Dalili
- Kungiyar ASUU ta umarci dukkanin mambobinta da su kauracewa shiga aji biyo bayan jinkirin biyan albashin Yuni 2025
- Tuni dai aka rahoto cewa malamai a jami'o'in Jos, ATBU, ABU da UniAbuja sun cika umarnin ASUU, inda suka daina shiga aji gaba daya
- Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna ya ce malamai ba za su koma bakin aiki ba har sai an biya albashin watan Yuni
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ƙarin rassan ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, sun sanar da dakatar da ayyukansu sakamakon jinkirin da gwamnatin tarayya ke yi wajen biyan albashin watan Yunin 2025.
A baya, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya shaida cewa ƙungiyar za ta fara aiwatar da tsarin “ba albashi, babu aiki” idan gwamnati ta jinkirta biyan albashi.

Kara karanta wannan
"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027

Source: Facebook
ASUU: Malaman jami'o'i sun janye ayyukansu
Yanzu haka, malamai daga jami’o’i daban-daban ba su sami albashin watan Yuni ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar malaman kwalejojin fasaha (ASUP) ta fitar da wata sanarwa a daren Lahadi tana barazanar tsunduma yajin aiki idan gwamnati ta ƙi sakin albashinsu.
Shugaban reshen ASUU na jami’ar Jos, Jurbe Molwus, ya tabbatar da cewa mambobin ƙungiyar sun dakatar da aiki saboda jinkirin biyan albashin watan Yuni.
Molwus ya ce wannan mataki ya biyo bayan umarnin majalisar zartarwa ta ƙasa na ASUU, wacce ta ba da damar ɗaukar matakin dakatar da aiki idan ba a biya albashi zuwa ranar uku ga wata ba.
Ya ƙara da cewa mambobin kungiyar sun daina shiga ajujuwa don koyar da darussa da kuma kauracewa halartar tarurrukan jami’a.
Ya kuma bayyana cewa malaman jami'a za su ci gaa da janye ayyukansu a duk lokacin da gwamnati ta gaza biyan albashi zuwa ranar uku ga kowane wata.

Kara karanta wannan
Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya
ASUU ta hana malamai shiga aji a ATBU
ASUU ta kuma fara aiki da ƙungiyar sa ido kan yajin aiki domin tabbatar da bin umarnin, a cewar wani rahoto na The Cable.
A Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, malaman ASUU sun daina shiga aji bayan reshen ASUU na ATBU ya fitar da sanarwa.
Shugaban reshen ASUU na jami’ar, Dr. Angulu Haruna, ya bayyana cewa jinkirin biyan albashin da gwamnati ke yi wata makarkashiya ce da aka kitsa da gangan.
“A kullum, albashinmu kan shiga cikin makon farko na wani wata mai kamawa. Muna ji muna kallo ana biyan sauran ma’aikatun gwamnati amma mu ban da mu.
“Idan muka tambaya, sai a ce wai saboda matsalolin sauya tsarin biyan albashi daga IPPIS ne, kawai muna ganin ana nuna fifiko ne ga wasu ma’aikatu fiye da mu.”
- Dr. Angulu Haruna.

Source: Facebook
Malamai sun ki shiga aji a UniAbuja, ABU
A jami’ar Abuja (UniAbuja), an gano cewa mafi yawan malamai sun kaurace wa aiki saboda rashin albashi, wanda ya sa dalibai suka rasa darussa da dama.

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
Wani malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce mafi yawan malaman jami'ar sun bi shawarar majalisar zartarwa ta ƙasa ta ASUU, inda suka dakatar da aiki har sai an biya albashin watan Yuni.
Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana cewa matakin na janye ayyuka martani ne kai tsaye kan wahalhalun da mambobin ASUU ke fuskanta sanadiyyar jinkirin biyan albashi.
Shugaban na ASUU ya ce sun dade suna fuskantar wannan matsala tun bayan da gwamnatin tarayya ta mayar da biyan albashin jami’o’i daga tsarin IPPIS zuwa GIFMIS.
ASUU da gwamnati sun fara tattaunawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta fara tattaunawa da ƙungiyar ASUU domin dakile shirin shiga yajin aikin da ke barazanar durƙusar da harkokin jami’o’i.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwa za su iya warware matsalolin cikin lumana da fahimta.
ASUU ta bayyana cewa idan har gwamnati ta gaza cika bukatunta, babu makawa za ta tsunduma yajin aiki domin kare muradun mambobinta.
Asali: Legit.ng